Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-01-24 17:42:39    
Kauyen Huaxi na kasar Sin

cri

A lardin Jiangsu dake kudancin kasar Sin,akwai wani kauye da ake kiransa `Huaxi`,mutanen kasar Sin sun mayar da shi a matsayin `kauye na farko na duniya`,wannan wuri yana da muhalli mai kyau kamar lambun shan iska da kamfanoni na zamani da motoci masu kyau da manyan dakunan kwana masu wadata,kowace rana,masu yawon shakatawa da suka zo daga wurare dabam daban na kasashen duniya sun zo kauyen Huaxi domin yin ziyara.Tun daga shekarar 1980,kauyen Huaxi ya zama `kauyen waya` da `kauyen babban daki` da `kauyen kananan motoci` da `kauyen inji mai kwakwalwa` na farko a nan kasar Sin.An kafa kauyen Huaxi a shekarar 1961,ya zuwa yanzu,shekaru 43 sun wuce.Ina dalilin da ya sa kauyen Huaxi ya kara samun wadatuwa a kwana a tashi?Game da wannan,mutanen kauyen Huaxi suna ganin cewa,dalilin da ya sa haka shi ne domin sun samu wadatuwa tare.

Tun bayan watan Yuni na shekarar 2001,sau uku ne kauyen Huaxi ya shigo da kauyuka goma sha biyar dake kewayensa a cikin Huaxi,ta yadda za su sami bunkasuwa tare.A halin da ake ciki yanzu,babban kauyen Huaxi ya hada da kananan kauyuka goma sha daya,fadinsa ya kai muraba`in kilomita 29,yawan mutanensa shi ma ya kara karuwa har ya kai dubu 28 da dari 6 da arba`in da biyu.Kwatankwacin yawan kudin da kauyen Huaxi zai samu a bana zai kai kudin Sin Yuan billiyan 20,wato ko shakka babu ya zama kauye na farko a duniya.

A shekarar 1961,yayin da aka kafa kauyen Huaxi,manoman kauyen Huaxi ba su samu wadatuwa ba,amma yanzu,bayan kokarin da aka yi a cikin shekaru arba`in da suka shige,fadin babban kauyen Huaxi ya karu da ninki 29,yawan mutanen kauyen ya karu da ninki 17.Game da wannan,Mr.Wu Renbao,tsohon sakataren kauyen da Mr.Wu Xieen,sakataren kauye na yanzu suna jin farin ciki.Mr.Wu Renbao ya bayyana cewa,babban kauyen Huaxi ya shigo da kananan kauyuka dake kewayensa a cikinsa,makasudinsa shi ne domin su samu wadatuwa tare.Mr.Wu Renbao ya ci gaba da cewa,mutum daya ko kauye daya ya sami wadatuwa,wannan ba shi da amfani sosai,muddin dai duk fadin kasar Sin ta samu wadatuwa,sai dukkan mutanen kasar Sin za su ji dadin zaman rayuwa tare.A cikin shekaru biyu da suka shige,kauyen Huaxi ya ware kudin Sin Yuan fiye da milliyan 74 da dubu dari bakwai don ba da taimakon kudi ga kauyuka dake kewayensa saboda su gina kadarko da hanyar mota da kuma aikin zaman jin dadin jama`a.Ban da wannan kuma,bi da bi ne kauyen Huaxi ya shirya ajin horo sau da yawa har ya kai dari daya ga sauran lardunan kasar Sin fiye da 20,wato yawan ma`aikatan hukuma da aka horar da su a kauyen Huaxi ya kai fiye da dubu goma,a sanadiyar haka,mutane fiye da dubu dari daya sun kubutar da kansu daga talauci.

Mr.Wu Renbao ya ce,abin da ya fi muhimmanci shi ne kimiyya.Dalilin da ya sa kauyen Huaxi ya ci nasara shi ne domin ya mai da hankali kan kimiyya.Kullum dukkan manoman kauyen Huaxi suna nacewa ga al`adarsu wato suna kishin jam`iyyar kwaminis ta kasar Sin da kasar Sin da kauyen Huaxi,kuma suna kishin iyalinsu da abokansu kuma suna kishin kansu.

Mr.Wu Xieen ya ci gaba da cewa,a halin da ake ciki yanzu,kauyen Huaxi yana samun sauye-sauye,amma makasudinsu na samun wadatuwa tare ba zai canja ba har abada.