Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-01-24 17:41:32    
Mutanen kasashen waje da ke nan kasar Sin

cri
Mutanen kasashen waje da suka zo yawon shakatawa a nan birnin Beijing , ko suna zaman rayuwa a nan birnin , Galibinsu suna son karamin titi na Beijing . Idan 'yan kasashen waje wadanda suka zo yawon shakatawa a nan birnin Beijing ba su kai ziyara a karamin titi ba , to ziyararsu ba ta sami cikakken sakamako ba . Idan sun sami dama , sun fi son kwana a mahasusin masaukin karamin titin . 'Yan kasashen waje masu yawa wadanda suke aiki ko suke karatu a nan birnin Beijing cikin dogon lokaci suna son zama a dakunan dake cikin karamin titin . Kwanan baya wakilin Rediyon kasar Sin ya kai ziyara a wani karamin titi mai suna Juer , inda ya gamu da wasu mutanen kasashen waje masu son zama a karamin titin birnin Beijing . Kananan titunan Beijing suna da tarihin fiye da shekaru 800 . Farfajiyoyin gargajiya dake cikin kananan tituna muhimman wurare ne da tsofafin mutanen Beijing ke zaman rayuwa . A nan ana kiyaye dabi'ar zaman yau da kullum da al'adun gargajiya na tsofafin mutanen Beijing kwarai da gaske . Titin Juer yana Unguwar Gabas ta birnin Beijing . Tsawonsa ya kai mita fiye da 400 . Shi wani tsohon titi ne wanda yake da tarihin shekaru fiye da 500 . A zamanin da manyan jami'ai da sarakuna sun taba zama a nan . Yanzu a cikin karamin titin akwai farfajiyoyin gargajiya masu yawa . Wadanan farfajiyoyin suna jawo hankulan mutanen kasashen waje .

A bakin titin , wakilinmu ya ci karo da Berna Hard , injiniya ne wanda ya zo daga kasar Jamus . Yana aiki a wata hukumar nazarin ilmin gine-gine ta Beijing . Lokacin da wakilinmu ya gan shi , ya je wajen ne don hayar dakin kwana . Mr. Berna ya ce , dalilin da ya sa ya zabi wannan wuri , shi ne yana kaunar halin musamman na karamin titin Beijing .

Mr. Berna ya ce , a ganina wannan wani wuri ne mai kyau kwarai da gaske . A cikin tsohon gini , bayan da aka yi gyuare-gyare , zaman yau da kullum na mazauna yana da sauki sosai . Titin ya riga ya zama wakilin gine-ginen Beijing , kuma ya zama wani kashi ne na tarihin Beijing .

Yanzu a Titin Juer yawan magidanta ya kai 200 . A cikinsu akwai iyalai kimanin 40 na mutanen kasashen waje . Sun zo ne daga kasar Ingila da kasar Amurka da kasar Fransa da kasar Jamus da kasar Isra'ila da sauran kasashe . A cikinsu akwai ma'aikatan kamfanonin kasashen waje da manema labaru kuma akwai dalibai da akawuna dake zama cikin 'yanci .

Baruh Kohen wani 'dan jarida ne na kasar Isra'ila . Kafin watanni 7 da suka shige ya zo nan birnin Beijing . Yanzu yana aiki a wata jaridar turanci ta Beijing . Ko da ya ke Mr. Kohen ya zo nan kasar Sin ba da dadewa ba , amma ya riga ya iya ma'amala da makwabtansa da sinanci .

Mr. Kohen ya ce , mazaunan dake wurin suna da zumunci sosai. Kullum suna murmushi , yayin da na ke hira da su da sinnanci ba sosai ba , kullum suna nuna zumunci da halin maraba . Hakan ya burge ni kwarai da gaske . Wannan dalili ne ya sa nake son zama a nan .

Mr. Kohen ya gaya wa wakilinmu cewa , a lokacin hutu yana son zuwa wani Dakin shan Kofi mai suna Xiaoxin . Matasa masu aikin hidima na Dakin su kan dafa kofi mai kauri gare ni har yana jin dadin zama kamar yadda yake cikin gidansa .

Mutanen kasashen waje dake zaune a Titin Juer na Beijing suna zaman jituwa da mazaunan wurin . In sun sami dama , sai su yi hira tare . Da sun gana da juna , sai kullum su yi gaisuwa cike da fara'a . Madam Zheng Fengying mai sayar da 'ya'yan itatuwa ta ce , bakin kasashen waje su kan zo wurinta don sayen 'ya'yan itatuwa . Su kan yi gaisuwa da ita . Ita kuma cike da farin ciki ta yi hira da su cikin zaman daidai wa daida .

Madam Zheng ta ce , wadannan 'yan kasashen waje suna da ladabi sosai . Kowa ya zo , sai ya yi gaisuwa da ni . Suna iya magana da sinnaci , sai mu yi hira da sauki . Wani lokaci kuma mun kara wasu maganganu .

Titin Juer da kewayansa akwai masaukai masu zaman kansu . Masu yawon shakatawa na kasashen waje su kan kai ziyara a wadannan masaukai . Wani masauki mai suna Qingzhuyuan dake kusa da titin Juer , ko da ya ke ba shi da girma wato yana da lambuna 30 , amma farashin dakin kwana a rana daya ya kai Yuan 210 kawai . Zhao Suhua , mai gidan masaukin ta gaya wa wakilinmu cewa , bakin kasashen waje sun cika a wajen .

To, jama'a masu sauraro , shirin "Zaman rayuwar Sinawa " da za mu iya kawo muku ke nan a yau . Ado ne ya shirya wannan shirin kuma ya fasara wannan bayanin, Jamilla ce ta karanto muku . Da haka muke muku sallama tare da fatan alheri .