Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-01-23 21:47:29    
Gidan ajiye kayayyakin gargajiya na tarihi na jihar Ningxia

cri

Jiya ran 7 ga wata, na iso birnin Yinchuan, babban birnin jihar Ningxia ta kabilar Hui mai ikon tafiyar da harkokin kanta. Bayan da na huta kadan kuma, na kai ziyara a Gidan ajiye kayayyakin gargajiya na tarihi na jihar Ningxia a yau ran 8 ga wata.

Wannan gidan ajiye kayayyakin tarihi yana da abubuwan tarihi na al'adu da ake gada daga kakanni kakanni na kasar Sin da yawa, amma abun da ta fi shaharra ita ce, Hasumiyar Chengtiansi, wadda take tsakiyar Gidan ajiye kayayyakin gargajiya na tarihi na jihar Ningxia.

An gina Hasumiyar Chengtiansi da tubali ne a shekarar 1050, wadda take da hawa 11, haka kuma tsayinta ya kai mita 64.5. sabo da tsayin haka, na sha wahala sosai, na hau kolin Hasumiyar Chengtiansi. Sa'an nan kuma, na ga dukkan gine gine da kayayyaki na birnin Yinchuan, wato sun yi kamar a karkashin kafofina. A kan kolinta, na ga itatuwa masu launin kuri a wannan Gidan ajiye kayayyaki, haka kuma na ga tsuntsaye da yawa suna cikin wadannan itatuwa.

Ban da Hasumiyyar Chengtiansi kuma, na kai ziyara a wani dakin da ke nuna fasahar rubuce-rubuce ta kwararre Wang Delin. Irin wadannan kalmomin da ya rubuta suna da ban sha'awa, wasu sun yi kamar dodanni, wasu sun yi kamar ruwa, wasu kuma sun yi kamar duwatsu.

Da na fito daga dakin da ke nuna fasahar rubuce rubuce, na kai ziyara a dakin gwada sababbin kayayyakin tarihi da aka same su ba da dadewa ba, da kuma dakin nuna kayayyakin al'adu na 'yan kabilar Hui ta kasar Sin. Lallai, Gidan ajiye kayayyakin gargajiya na tarihi na jihar Ningxia ya zama wani babban banki da ake ajiye kayayyakin al'adu da na tarihi na jihar Ningxia baki daya.

A gefen Gidan ajiye kayayyakin gargajiya na tarihi na jihar Ningxia kuma, yana kasancewa da wasu kantunan da ke musanyar kayayyakin al'adu da fasaha, da kuma wani babban gida da ke kira 'birnin kayayyakin tarihi'. A wadannan wurare kuma, na fahimci al'adun Ningxia sosai, wadanda suke zama wani muhimmin sashe na al'adun gargajiya na kasar Sin.(Danladi)