Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-01-23 21:42:56    
Abincin musulmai da likitancin gargajiya na kabilar Hui a jihar Ningxia

cri

Da sassafe kuma, na tashi daga hotel, na nufi Kamfanin abincin musulmai mai suna 'Jinfulai' a cikin Sinanci. Magaja na wannan kamfani wato Mr Ma Honglin ya raka mana, mu zagaya a cikin kamfaninsa. A wurin kuma, an yanka awaki bisa oda, wato bayan da aka yanka awakin, a kan wanka su, sa'an nan kuma, a kan yi naman awaki iri daban daban. Manaja Ma ya gaya mana cewa, ya riga ya yi shekaru fiye da goma yana sha'anin naman awaki, domin samara da abinci mai dadi ga musulmai a jihar Ningxia.

Bayan da na gama ziyara a Kamfanin abincin musulmai mai suna 'Jinfulai', sai karfe biyu na yamma ya yi, nan da nan ne, na kai ziyara a wani kamfani daban na musulmai, wato mai suna 'Houshengji' a cikin Sinnanci. Hedkwatar kamfanin 'Houshengji' yana birnin Shanghai na kasar Sin. Wannan kamfani ya mai da hankali sosai kan abinci musulmai, sabo da haka ne, ya kafa wani reshen kamfanin musulmai a jihar Ningxia. A halin yanzu dai, kamfanin ya ba da taimako sosai ga bunkasuwar tattalin arziki ta jihar Ningxia.

Bayan da na gama ziyara a kamfanoni biyu na abincin musulmai, na ziyarci wani wurin al'adu, wato gidan likitancin gargajiya na kabilar Hui, wanda sunansa shi ne 'Tangpingbazhen' a cikin harshen Sinanci. Fasahar 'Tangpingbazhen' ta likitancin gargajiya ta kabilar Hui tana daya daga cikin abubuwan tarihi na al'adu da ba na kayayyaki ba, da ake gada daga kakanni kakanni na kasar Sin. Na dauki hoto tare da manaja Yang Huaxiang domin masu karanta shafinmu na internet ku gani.(Danladi)