Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-01-23 16:14:08    
Idan mata masu ciki suna cin abincin gina jiki, to jariransu za su samu lafiyar jiki

cri

Kamar yadda Sinawa su kan ce, idan ana cin apple guda a ko wace rana, to ba za a bukaci ganin likita ba. Yanzu wani sabon binciken da aka gudanar ya shaida wannan magana, wanda ya gano cewa, idan mata suna cin appale mai yawa lokacin da suke da ciki, to zai iya kare yaransu daga cutar tarin asthma a lokacin yarantakarsu.

Manazarta na kasar Holland da na sauran kasashe sun bayar da wani rahoto a kan mujallar Thorax ta kasar Amurka, cewa sun gudanar da wani bincike ga mata masu ciki kusan 2000 wajen abincin da su kan ci, daga baya kuma sun zabi yara 1253 da suka haifa domin ci gaba da gudanar da bincike gare su wajen wane irin tasiri ne al'adar cin abinci ga mata masu ciki zai bai wa yaransu a fannin hanyoyin numfashi.

Kuma manazarta sun bayyana cewa, binciken ya gano cewa, game da mata da su kan ci appale da yawa lokacin da suke da ciki, yiyuwar kamuwa da cutar tarin asthma ga yaransu ta yi kadan. Dalilin da ya sa haka shi ne watakila sabo da apple yana kunshe da wani sinadarin musamman, kamar sinadarin flavoid da dai sauransu.

To, jama'a masu sauraro, shirinmu na yau na ilmin zaman rayuwa ke nan. Muna fatan kun ji dadinsa, da haka Kande ce ke shirya muku wannan shiri kuma ke cewa mako gobe war haka idan Allah ya kai mu.(Kande Gao)


1 2