Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-01-23 16:12:58    
Malam Er Yuehe, mawallafin kagaggen labarin tarihi na kasar Sin

cri

Malam Er Yuehe yana da shekaru sama da 50 da haihuwa a bana, an haife shi ne a lardin Shanxi da ke a arewacin kasar Sin. Amma ya dade yana aiki da zaman rayuwarsa a lardin Henan da ke a tsakiyar kasar Sin.

Malam Er Yuehe ya fara rubuta kagaggen labari ne a shekarar 1986, yayin da yake da shekaru 40 da 'yan doriya da haihuwa. Kagaggen labari mai suna " Kang Xi, sarkin kasar Sin a zamanin daular Qing ya zama na farko da ya wallafa. Yawan babbaku na wannan kagaggen labari ya kai miliyan 1.5. A cikin kagaggen labarin nan, an yi bayani a kan Kang Xi, sarkin kasar Sin a zamanin daular Qing yau da shekaru 300 da suka wuce. Wannan kagaggen labari da Malam Er Yuehe ya wallafa ya sami martani sosai daga wajen masu aikin adabi na kasr Sin, haka nan kuma wasu kagaggun labaru biyu da ya wallafa kamar su "Yong Zheng, sarkin kasar Sin a zamanin daular Qing ", da "Qian Long, sarkin kasar Sin a zamanin daular Qing" su ma sun sami karbuwa sosai daga wajen masu karatu. Da Malam Er Yuehe ya tabo magana a kan kagaggen labari da ya wallafa, sai ya bayyana cewa, "mu mawallafa ma muna cin gajiyar manufar yin gyare-gyare da bude wa kasashen waje kofa wajen wallafa kagaggen labarinmu, yanzu ba mu damuwa da hana mu rubuta abubuwa. Burinmu shi ne wallafa kagaggun labaru nagartattu domin gamsar da masu karatu. Abin da ya fi muhimmanci gare mu shi ne neman samun karbuwa daga wajen masu karatu a yanzu da nan gaba,"

Yayin da yake samartaka ne aka yi babban juyin juya halin al'adu a kasar Sin, sabli da haka Malam Er Yuehe bai taba samun damar shiga jami'a ba. Ya taba yin aikin hakar kwal da na gina gidaje da shimfida hanyoyi da sauransu. Ban da wadannan kuma ya shafe shakaru 10 yana aikin soja. Daga wadannan ayyuka da ya yi ne, ya sami babban burinsa. Ya nace ga yin karatu, musamman ma yana sha'awar littattafan tarihi ainun. Malam Er Yuehe ya waiwayi cewa, "da na fara yin rubutun kagaggen labari, na kan yi aiki mai yawa a rana, bayan da na tashi daga aikina, na koma gida, na kan yi rubutu-rubutu har zuwa daddare. Musamman ma a lokacin zafi, na kan yi gumi shar ban sabo da ba ni da fanka a gida, kuma ga sauro. Amma duk wadannan wahalhalu ba su hana ni rubuta kagaggen labari ba. "

Malam Er Yuehe ya iya samun sakamako mai kyau wajen wallafa kagaggun labaru duk bisa matukar kokari da ya yi. A lokacin da yake rubuta kagaggen labari mai suna "Qian Long, sarkin kasar Sin a zamanin daular Qing", ya kamu da ciwon shanyawar jiki, amma abin farin ciki shi ne an ceci ransa daga ciwon nan. Ya kammala aikin wallafa wannan kagaggen labari ne yayin da yake kwance a asibiti.

Ban da rubutun kagaggen labari, Malam Er Yuehe yana sha'awar tattara kan sarki ainun. Yau da shekaru 30 ke nan yake tattara kan sarki. A duk lokacin da ya gaji da rubutunsa, sai ya dauki littattafan kan sarki, ya dudduba, ya ji dadi.

'Yan iyalin Malam Er Yuehe suna jin dadin zamansu kwarai. Matarsa da diyarsu su ma suna da aikin yi. Da ya tabo magana a kan zaman rayuwarsa, sai Malam Er Yuehe ya bayyana cewa, "mawallafa farar hula ne. Na kan gudanar da harkokina daidai kamar yadda farar hula ke yi. Amma lokaci ya kan kure mini. A hakika dai, na kan yi aiki tukuru. Ba safai na kan yi wasan dara da na kati ko yin hira tare da aminaina a kan abubuwa da muke rubutu ba.

Ko da yake Malam Er Yuehe shahararren mawallafi ne a fannin tarihi, amma yana lura da abubuwa da ke faruwa a kasar Sin, ya sha ware kudin shiga da ya samu daga wajen wallafawar littattafansa don ba da taimako ga makarantun firamare wadanda ke fama da karancin kudi. Manufar da yake neman cim ma shi ne kafa makarantun firamare biyar bisa taimakon kudinsa a wurare da ake fama d taulauci a kasar Sin. (Halilu)