Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-01-22 18:14:10    
Dakin wasa na ma'aikata na Beijing

cri

Bayan da kuka fita daga kofa ta arewa ta wannan filin wasa, ku ci gaba da zuwa yamma na tsawon mita 500, za ku isa wurin da za a yi shirin wasan dambe na gasar wasannin Olympic ta Beijing, wato dakin wasa na ma'aikata na Beijing.

Bayan da aka kammala kafa dakin wasa na ma'aikata na Beijing a shekarar 1961, har kullum an mayar da shi a matsayin wani muhimmin wuri a Beijing, inda a kan shirya manyan harkoki a ciki. Bisa shirin da aka tsara game da yin masa kwaskwarima a wannan karo domin share fagen gasar wasannin Olympic ta Beijing, ba a canza siffar dakin wasan da kuma tsarin gininsa ba, sai a sake tsabatacewa da kuma kayatar da shi kawai, har ma ba a canza abubuwan ado da aka yi wa kofofinsa ba. Shi ya sa a idanun mutanen da suka kallaci dakin wasa na ma'aikata, ko kusa ba su ji mamaki kan wannan dakin wasa bayan da aka yi masa kwaskwarima.

Babban canjin da dakin wasa na ma'aikata ya samu bisa kwaskwarima a wannan karo ita ce canza tagoginsa. A da an hada tagogin da aka kera da sanholo a dakin wasa na ma'aikata, amma yanzu irin wadannan tagogi ba su iya tabbatar da ma'aunin yin tsimin makamashi da kiyaye muhalli ba, shi ya sa an canza dukkansu, sabbin tagogin sanholo da ke da tagwayen gilas sun maye gurbinsu domin kiyaye muhalli. Irin wannan taga ta hada da tagwayen gilas, an kuma zuba iskar musamman a tsakanin wadannan tagwayen gilas, ta haka an iya hana amo ya shiga dakin wasan. An gina dakin wasa na ma'aikata a dab da wata muhimmiyar hanya a Beijing. Da rana, motoci na kaiwa da dawowa. Ko da da dare kuwa, shahararren titin Guijie da ke kusa da wannan dakin wasa ya cunkushe da mutane, domin wannan titi ya yi suna ne saboda dakunan cin abinci manya da kanana da ke cikin titin suna samar wa masu sha'awar cin abinci abinci mai dadin ci iri daban daban. Bayan da aka hada sabbin tagogi a dakin wasa na ma'aikata, ko ana kara sosai a waje da dakin wasan, amma an yi tsit a cikin dakin wasan. Bugu da kari kuma, irin wannan taga ya iya kiyaye zafi a cikin wannan dakin wasa. Yin amfani da irin wadannan tagogi wajen dumama daki ya iya yin tsimin makamashi mai yawan kusan kashi 50 cikin kashi dari.

Mai kula da aikin kwaskwarima ya yi karin bayani cewa, baya ga sabunta dukkan injunan shakar iska da ba da haske da samar da wutar lantarki, an kuma kara samar da kujeru 240 ga manema labaru da kuma wasu fiye da 30 ga manyan baki da kuma wani dakin hutu mai fadin murabba'in mita 40 ga manyan baki a cikin dakin wasa na ma'aikata. Don haka, an fi mayar da mutane a gaba da kome a dakin wasa na ma'aikata, kuma an fi tabbatar da ingancin dakin wasan, haka kuma, mutane sun fi jin dadi a cikin wannan dakin wasa.

In wani ya hango daga nesa, sai ya ga filin wasa na ma'aikata da dakin wasa na ma'aikata suna makwabtaka da juna, sun kuma kara wa juna kyan gani. Bayan da aka yi musu kwaskwarima a watan Agusta na shekarar 2007, dukkansu sun sabunta siffofinsu, sun nuna wa mutane sabbin siffofinsu na zamani.