Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-01-22 16:54:39    
Kasar Sin ta dauki matakai domin tinkarar yanayi mai tsanani

cri

A cikin kwanakin baya, an yi sanyi sosai da kankara mai laushi a yawancin yankunan kasar Sin. A ran 21 ga wata, gwamnatin kasar Sin ta ba da wata sanarwa inda ta bukaci hukumomin yankunan kasar da su kare rayuwar jama'a da duniyoyyinsu da tsarin aikin kawo albarka da zaman rayuwa, domin ta haka za a rage yawan hasara.

Tun ran 15 zuwa ran 21 da yamma ga wannan wata, an yi mahaukaciyar kankara mai laushi a lardin Hu'nan da ke tsakiyar kasar Sin, a sakamakon haka, an sami matsala wajen samar da wutar lantarki. Daga ran 20 zuwa ran 21, lardin Sichuan da ke yammacin kasar Sin ya samu mahaukaciyar kankara mai laushi, wadda ta haddasa matsala kan zirga-zirga sosai.

Gwamnatin kasar Sin ta bukaci yankunan kasar dabam daban da su tafiyar da tsarin gaggawa na zirga-zirga. Kuma ya kamata hukumomin da abin ya shafa su gyara manyan gine-gine cikin lokaci domin ba da tabbaci wajen samar da ruwa, da wutar lantarki, da iska mai dumama daki, da hanyoyin sadarwa. Ban da haka kuma, ta bukaci yankunan inda aka yi mahaukaciyar kankara mai laushi da su kara zuba jari domin tinkarar bala'in da kuma daidaita zaman rayuwar jama'a yadda ya kamata.