Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-01-22 08:37:21    
Gasar wasan kwallon hannu bisa gayyata ta Goodluck Beijing ta daukaka bunkasuwar wasan kwallon hannu a kasar Sin

cri
A farkon kwanaki 10 na wannan wata, an yi gasar wasan kwallon hannu bisa gayyata ta Goodluck Beijing a dakin wasan kwallon hannu na cibiyar wasanni ta wasannin Olympic ta Beijing da kuma dakin wasa na kasar Sin domin yi gwajin wadannan dakunan wasa 2 a fannonin na'urori da shirya gasa da kuma ba da hidima ga kafofin yada labaru da tsaron lafiyar mutane.

Ko da yake kungiyoyin wasan kwallon hannu masu shiga gasar dukkansu sun zo daga kasasr Sin, babu kungiyoyin ketare da suka shiga gasar, amma bisa yawan 'yan kallo a dakunan wasa, 'yan kallo sun kara mai da hankulansu kan gasar wasan kwallon hannu, sun kuma kara nuna sha'awarsu kan wannan wasa. Dimbin mutane sun bayyana fatansu na cewa, ta hanyar shirya wannan gasa da kuma gasar wasannin Olympic ta Beijing, wasan kwallon hannu a kasar Sin zai bazu a kasar Sin, zai zama wani irin wasa da dimbin mutane suka shiga ciki.

Malam Liu Xiaoli, wani mai kishin wasan kwallon hannu ya je kallon gasar wasan kwallon hannu bisa gayyata ta Goodluck Beijing a ko wace rana, ya gaya mana cewa, a maimakon a fi mai da hankali kan zakara, kyan ganin wasan kwallon hannu ya janyo hankalinsa. Ya ce,'Ina tsammani cewa, wasan kwallon hannu na da matukar sha'awa. 'Yan wasa su kan kai wa juna hari cikin sauri. Ya yi kama da hada sigogin musamman na wasan kwallon kafa da kwallon kwando tare. 'Yan wasa su kan kai hari da kuma tsaron gidansu cikin sauri, sun kuma jefa kwallo da yawa. A takaice dai, ina matukar sha'awar kallon gasar wasan kwallon hannu. In wasan kwallon kafa da kwallon kwando sun yi farin jini sosai, to, wasan kwallon hannu ba zai gamu da matsala ba, zai sami karbuwa a kasar Sin. Ina fatan kasar Sin za ta yada wannan wasa. Na yi imani da cewa, tabbas ne dimbin mutane za su amsa kiran gwamantin.'

Kazalika kuma, gasar da aka yi a wannan karo ta sanya masu aikin sa kai su kara saninsu kan ka'idoji da hanyoyin gasar wasan kwallon hannu, sun kara ba da hidima mai kyau. Yan Da, wani dalibi a Beijing, ya yi aikin sa kai a cikin dakin wasan kwallon hannu na cibiyar wasanni ta wasannin Olympic ta Beijing a wannan karo. A matsayin mai kishin wasan kwallon kwando, Yan Da ya kara nuna sha'awa kan irin wannan wasa mai yawan fasahohin wasan kwallon kwando, ya kuma lakanci ka'idojin wasan cikin sauri. Ya ce,'A ganina, wasan kwallon hannu na da dadin kallo sosai, sa'an nan kuma, shi da wasan kwallon kafa da na kwallon kwando sun yi kunnan doki bisa yin takara mai tsanani da fasahar 'yan wasa. Wani wasa ba zai sami ci gaba mai dorewa ba, sai yana kasancewa da tushe mai inganci a tsakanin mutane. Ga misali, wasan kwallon kafa ya yi farin jini a kasar Brazil, wasan kwallon tennis ya sami karbuwa sosai a Sin. shi ya sa wajibi ne a fadakar da fararen hula da wasan kwallon hannu, ta haka za su fara kishin wannan wasa.'

Kowa ya sani cewa, samar da tushe mai inganci a tsakanin mutane ya fi muhimmanci wajen raya wani wasa. A cikin kasashen Turai da yawa da ke kan gaba a duniya a wasan kwallon hannu, wasan kwallon hannu ya zama na biyu da mutane ke kishin shiga a ciki a kungiya-kungiya bayan wasan kwallon kafa. Bugu da kari kuma, an sha shirya gasanni a tsakanin kungiyoyi da kungiyoyi da kuma a tsakanin yankuna, shi ya sa wadannan kasashe suka kiyaye matsayinsu a kan gaba a duniya. Amma a kasar Sin kuwa, ba a iya nuna fara'a kan makomar wasan kwallon hannu ba. Malam Peng Ning, shugaban sashen wasan kwallon hannu na cibiyar wasan kwallon gora a fili da wasan kwallon baseball da wasan kwallon softball ta hukumar wasanni ta kasar Sin ya yi karin bayani cewa,'A kasarmu, ba a kasancewa da kyakkyawan tushe a tsakanin mutane ta fuskar wasan kwallon hannu. Yawancin 'yan wasan kwallon hannu ba su sami aikin horaswa na wasan kwallon hannu tun daga yarantakarsu ba. 'Yan wasanmu na yanzu dukkansu su ne 'yan wasan kwallon kwando a da. Saboda ana karancin kudi, kuma ba mu da cikakken tsarin horar da 'yan wasa matasa, shi ya sa da kyar mu kyautata makinmu.'

Amma duk da haka, sha'warar da 'yan kallo suka nuna kan gasar wasan kwallon hannu bisa gayyata ta Goodluck Beijing ta sanya malam Peng ya ji farin ciki sosai, ya ce,'A gaskiya gasar wasan kwallon hannu na da matukar dadin kallo. Amma saboda ba mu kan gaba a duniya ba, shi ya sa wannan wasa bai yi farin jini a kasar Sin ba tukuna. Matukar sha'awa da 'yan kallo suka nuna a cikin gasar Goodluck Beijing a wannan karo ta faranta mana rai sosai. In mutane sun ci gaba da nuna sha'awarsu, to, a ganina, nan gaba kasar Sin za ta sami babbar nasara a wasan kwallon hannu.'(Tasallah)