Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-01-21 17:20:02    
Kasar Sin ta kara karfinta wajen yin bincike da bunkasa sana'ar kira cikin cin gashin kai

cri

Yau ran 21 ga wata a nan birnin Beijing, Mr. Cai Weici, mataimakin shugaban hadaddiyar kungiyar sana'ar kanikanci ta kasar Sin ya bayyana cewa, kasar Sin ta samu babban ci gaba wajen bincike da kera manyan injuna, tana kara kwarewa wajen bincike da bunkasa sana'ar kira cikin cin gashin kai, kuma ta ba da babban taimako don sa kaimi ga ci gaban tattalin arzikin kasa da kyau kuma da sauri, haka kuma ta aza harsashi mai inganci domin bunkasa sana'ar kera manyan injuna a shekarar 2008.

A gun taron manema labaru da aka yi a yau kan harkokin sana'ar kanikanci da aka gudanar da su a shekarar da ta wuce, Mr. Cai Weici ya bayyana cewa, a shekarar da ta wuce an gudanar da manyan tsare-tsaren gwamnatin kasar Sin a fannin masana'antar kanikanci dangane da raya sana'ar kira, an dukufa kan aikin yin kirkire-kirkire cikin gashin kai, kuma an bullo da wani kyakkyawan halin fitar da kayayyakin masana'antar da kuma sayar da su. Jimlar kudin da aka samu a shekarar 2007 daga wajen sana'ar kanikanci a karo na farko ne za ta wuce kudin Sin wato Yuan biliyan 7000, wato ta karu da kusan kashi 32 cikin 100 bisa ta shekarar bara waccan, kuma saurin karuwar da aka samu ya wuce kashi 20 bisa 100 cikin jerin shekaru 5 da suka wuce. Mr. Cai ya bayyana cewa, "Kasar Sin ta samu babban ci gaba a shekarar 2007 daga fannoni da yawa wajen bincike da kera manyan injuna, wato ta samu wasu sabbin sakamako wajen tsimin makamashi da rage yawan abubuwan kazanta da ake zubarwa. Yawan kanikancin da aka fitar cikin cin gashin kai ya wuce kashi 80 bisa 100, sabo da haka an ba da taimako yadda ya kamata don sa kaimi ga bunkasa tattalin arzikin kasa da kyau kuma da sauri."

Cikin samfurorin muhimman kayayyaki 95 da aka fitar a shekarar bara wajen sana'ar kanikanci, kashi 2 bisa 3 wandada saurin karuwarsu ya wuce kashi 10 bisa 100. Da akwai muhimman kayayyaki da yawa wadanda suka samu ci gaba wajen yawansu da aka fitar, alal misali, an kimmanta cewa, yawan na'urori irin na zamani da aka fitar a duk shekarar zai wuce dubu 120, wato ya karu da dubu 35 bisa na bara waccan.

Mr. Cai Weici ya bayyana cewa, cikin shekarar da ta wuce, an samu ci gaba lami lafiya wajen kafa tsarin yin kirkire-kirkire cikin gashin kai wanda aka maida kasuwanni a matsayin jagorancinsa, wanda kuma aka yi ta hanyar hada aikin kawo albarka da yin bincike. A kan wannan Mr. Cai ya ce, "A shekarar 2007, an yi ta samun nasarori wajen fitar da injuna masu yin tsimin makamashi da rage yawan abubuwan kazanta da ake zubarwa, da injuna domin muhimman sana'o'i, da manyan na'urori na zamani, ana nan ana yin yunkurin fitar da sabbin kayayyaki, kuma an samu takamaiman karfi wajen sana'ar kira."

Da a waiwayo shekarar 2007, ana iya ganin cewa wasu masana'antu suna cikin kyakkyawan yanayi wajen kera injuna, wato sun samu babban ci gaba wajen fasaha da ingancin kayayyaki, kasuwannin da suka samu sai kara fadadawa suke.

Lokadin da Mr. Cai ya sa ido kan shekarar 2008 ya ce, an kimmanta cewa, saurin karuwar da za a samu a wannan sabuwar shekara zai wuce kashi 20 bisa 100 cikin jerin shekaru 6.  (Umaru)