Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-01-21 16:34:48    
Birnin Beijing Ya Himmatu Domin Gudanar Da Wasannin Olympics Cikin Nasara

cri

Ma Zhenchuan shugaban hukumar tsaro ta Beijing ya bayyana cewa, birnin na Beijng ya himmatu domin gudanar da wasannin Olympics cikin nasara da cikakken tsaro.

Shugaban na hukumar tsaron ya kara da cewa, ana sane da shirin masu harin ta'addanci. na kai hare-hare a lokacin Olympics, saboda haka hukumarsa ta tanadi hanyoyi daban-daban domin kare mahalarta gasar wasannin. Wato hakan ya sa dole ne a ba da kyakkyawan tsaro a birnin na Beijing domin a gudanar da wasannin cikin nasara.

Tun daga watan Janairu zuwa watan Mayu, 'yan sandan Beijing za su fadakar da jama'a irin ayyukansu dangane da kyautata tsaro, da ba da kariya daga kashe-kashen kai, fashi da makami, da kuma kwace mugayen makamai kamar bindigogi, wukake da kuma kwari da baka.

Bugu da kari, 'yan sandan sun fara kai samame wuraren shakatawa domin hana tambola da kuma nuna finafinai na tsiraici da batsa. Haka kuma sun jaddada cewa za su iya kawar da duk wani abu mai hadari daga kimanin mita 200 na wuraren da ake gudanar wasannin. ( Yakasai )