Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-01-21 16:09:32    
Wasu labaru game da kabilun kasar Sin

cri
---- Kwanan baya gwamnatin jihar Mongoliya ta gida mai ikon tafiyar da harkokin kanta ta kasar Sin ta kaddamar da wata takardar inganta aikin ba da ilmin kabilu wadda a ciki aka gabatar da cewa, nan gaba za a gina gidajen renon yara na gwamnati a wuraren da 'yan kabilar Mongoliya masu yawa ke zama, wadanda kuma za su yi aikin koyarwa da harshen kabilar Mongoliya.

An ce, gwamnatin jihar ta nemi da a gina wani gidan renon yara na gwamnati wanda ya dauki harshen kabilar Mongoliya a matsayin muhimmin harshensa wajen aikin koyarwa a kowace gunduma da kowane gari inda hukumomin gwamnatin yankuna da na gundumomi suke, inda kuma 'yan kabilar Mongoliya masu yawa ke zama, a sauran wuraren da ba su da sharudan kafa irin wadannan gidajen renon yara kuma, za a iya bude kos din share fagen shiga firamare ga kananan yara cikin makarantun firamare na kabilu. A sa'i daya kuma gwamnatin ta ware kudi domin gudanar da aikin koyarwa na wadannan gidajen renon yara.

---- Kwanan baya a nan birnin Beijing, an yi bikin ba da kyautar kayayyakin asibiti domin yaki da talauci da kiwon lafiya, ofishin yaki da talauci na asusun hana kwararowar hamada na kasar Sin da gundumar Honghe ta kabilar Hani da ta Yi da ke lardin Yunnan ta kasar su ne suka shirya wannan biki tare, yawan darajar kayayyakin asibitin da aka bayar ya wuce kudin Sin wato Yuan miliyan 26.

Mr. An Chengxin, direktan asusun hana kwararowar hamada na kasar Sin ya bayyana cewa, asusun nan wani sashe ne da aka kafa bayan samun amincewa daga majalisar gudanarwa ta kasar kuma bisa makasudin samun moriyar jama'ar duk kasa baki daya. Asusun nan kuma yana dukufa kan aikin cimma daidaito kan kwararowar hamada, da farfado da kuma raya kakkyawan muhallin halittu masu rai. Ban da wannan kuma asusun ya ba da taimako domin bunkasa harkokin likitanci da kiwon lafiya da ake yi a wurare masu fama da talauci na kasar Sin. Yanzu asusun nan yana gudanar da ayyuka da yawa domin samun moriyar jama'a a larduna Gansu da Guizhou da Hebei da kuma jihar Mongoliya ta gida mai ikon tafiyar da harkokin kanta na kasar Sin.

---- Kwanan baya, kauyawa na wani tsohon gari na kabilar Dai da ke lardin Yunnan na kasar Sin sun kammala aikin rubuta wani littafi mai suna "Tarihin Mengma" wanda aka rubuta musamman domin bayyana al'adu da zaman rayuwar 'yan kabilar Dai na kasar Sin, za a sayar da wannan littafi daga watan Afril na shekara mai zuwa. A cikin wannan littafi, an bayyana cikakken tarihin sauye-sauye da kuma ci gaban da aka samu a tsohon garin Mengma na kabilar Dai wanda ya yi shekaru kusan 100 da ginuwa.

An ce, Littafi mai suna "Tarihin Mengma" wanda aka shirya ta bakunan tsofaffi 'yan kabilar Dai fiye da 30 na garin Mengma na gundumar Menglian ta lardin Yunnan, wanda ya fi tsufa daga cikin wadannan tsofaffi ya ba shekkaru 86 baya. Littafin nan ya bayyana fannoni daban-daban na zaman rayuwa da al'adun kabilar Dai bisa gaskiya, yawan kalmomin da aka rubuta cikin littafin ya wuce dubu 80.