Ran 21 ga wata Mayu na shekarar bara rana ce mai muhimmanci ga Malam Kamal Sanusi, dan kasar Malasiya. A wannan rana, an kaddamar da wata Hotel din Sheraton Guihang a birnin Guiyang, fadar gwamnatin lardin Guizhou da ke a kudu maso yammacin kasar Sin. Malam Kamal Sanusi kuma ya zama mataimakin babban manaja na wannan hotel. Da Malam Kamal Sanusi ya sauka a birnin Guiyang, sai ya fara kaunarsa. Ya ce, "ina kaunar lardin Guizhou musamman birnin Guiyang kwarai. Da na sauka a birnin Guiyang, sai na fara kaunarsa. Ga mutane da yawa na kai da kawowa a cikin birnin. In dare ya yi, a kan kayatar da birnin da kyau, kayayyakin abinci da ake samu a birnin sun yi iri-iri, musamman ma da dare, a kan sayar da abincin gargajiya na birnin iri daban daban wadanda ke da dacin ci ainun. "
Ko da yake Hotel din sheraton Huihang yana unguwar kasuwanci inda mutane da yawa ke kai da kawowa, amma Kamal Sanusi ya ce, idan an son kara neman samun ci gaba wajen raya Hotel dinsa a lardin Guizhou, to, kamata ya yi, a mayar da hotel da ya zama hotel mai sigar musamman na lardin Guizhou. Ya kara da cewa, "bisa matsayinsa na babban hotel iri na duniya na farko da aka kafa a lardin Guizhou, wajibi ne, mu mayar da hotel dinmu da ya zama hotel mai sigar musamman na wuri. Za mu bi sabuwar manufar ba da hidima a cikin hotel, ta yadda hotel dinmu zai shahara a wurin"
A cikin shekarun nan da suka gabata, an yi kokari sosai wajen bunkasa harkokin yawon shakatawa a lardin Guizhou. Yawan masu yawon shakatawa na gida da waje wadanda suka yi yawon shakatawa a lardin Guizhou ya wuce miliyan 47 a shekarar 2006. Jimlar kudin da lardin ya samu ta kai kudin Sin Renminbi Yuan biliyan 38.7. Ko shakka babu. duk wadannan albishiri ne ga Kamal Sanusi wanda ke kula da Hotel. Da malam Kamal Sanusi ya tabo magana a kan wannan, sai ya bayyana cewa, " wannan ba ma kawai albishiri ne ga lardin Guizhou da birnin Guiyang ba, har ma Hotel din Sheraton. Mutane da yawa sun zo nan sun yi yawon shakatawa, wannan ya samar da kyakkyawar dama ga lardin Guizhou. Amma wani batun da ya kamata mu yi la'akari da shi sosai, shi ne, yaya a yi amfani da damar da aka samu wajen bunkasa harkokin yawon shakatawa don kara raya lardin Huizhou da kyau?"
Malam Kamal Sanusi yana cike da imani sosai ga bunkasa harkokin hotel dinsa a lardin Guizhou. Ya ce, ko da yake a da lardin Guizhou yana fama da talauci, amma tun bayan da ta fara aiwatar da manufar bude kofarta ga gida da waje, kwararru na wurare daban daban na kasar Sin da 'yan kasuwa na kasashen waje da yawa sun runtuma zuwa lardin Guizhou don neman samun damar bunkasa harkokinsu. A ganinsa, yanzu ana bunkasa harkokin kasuwanci cikin sauri a lardin Guizhou, alal misali ci gaba da ake samu wajen bunkasa harkokin sadarwa da na kera motoci da wuraren cin abanci ya zama ishara ga ci gaba da ake samu wajen raya lardin Guizhou cikin sauri. Ya hakake cewa, nan gaba ma za a kara raya lardin Guizhou cikin sauri sosai har cikin wani dogon lokaci.
Ya zuwa yanzu, Malam Kamal Sanusi ya riga ya shafe wasu watanni yana aiki a birnin Guiyang. Abubuwa da suka shaku cikin zuciyarsa, su ne, birnin Guiyang birni ne mai ban sha'awa, kuma wuri ne mai jin dadin zama. Idan an tambayi Malam Kamal Sanusi cewa, yaya lardin Guizhou yake?, zai iya amsa cikin Sinanci cewa, "lardin Guizhou yana da kyaun gani sosai, yanayinsa yana da kyau kwarai, mutanensa kuma na nuna aminci sosai." (Halilu)
|