Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-01-21 15:34:34    
An Kaddamar Da Tufafin Musamman Domin Amfanin Ma'aikata Da Masu Bada Taimako A Lokacin Wasannin Olympics

cri
A ranar lahadi da ta gabata ne aka kaddamar da tufafin musamman domin amfanin ma'aikata da kuma masu ba da taimako a lokacin wasannin olympics. An kaddamar da tufafin ne domin murnar sauran kwana 200 a fara wasannin na Olympics,

Domin kawata wadannan tufafi, an yi amfani da launi kwatankwacin na wutar yula da za a yi amfani da ita wajen bude gasar wasannin. Su kuma ma'aikata suna da tufafi masu launin ja, yayin da masu bada taimako za su yi amfani da tufafi masu launin shudi. Sauran masu kula da tafiyar da wasannin kuma za su yi amfani da tufafi masu launin toka-toka.

Wadanda suka tsara wadannan tufafi dai wakilai ne daga sashen al'adun gargajiya na kwamitin shirya Olympics (BOCOG), da makarantar saka tufafi ta Beijing, da cibiyar fasaha ta jami'ar Tsinghua, da kuma cibiyar fasahar zane-zane ta kasar Sin.

Bugu da kari BOCOG ta ba da tabbacin cewa kimanin mutane 130,000 ne za su sami tufafin wasanni na hamshakin kamfanin kasar Jamus. Za a gudanar da gasar wasannin na Olympics ne daga 8-24 na watan Agusta. ( Yakasai )