
Ran 21 ga wata, rana ce da ta rage sauran kwanaki 200 da bude gasar wasannin Olympic ta Beijing. Bisa kididdigar da aka samu daga ofishin jagorantar ayyukan gine-gine domin gasar wasannin Olympic ta Beijing ta shekarar 2008, an ce, a cikin dukkan filayen wasa guda 37 na gasar wasannin Olympic ta Beijing, ban da filin wasa na kasar Sin wato Shekar Tsuntsaye, an kammala dukkan sauran 36 cikin lokaci, sa'an nan kuma, za a yi gwajinsu ta hanyar shirya jerin gasanni na 'fatan alheri a Beijing'.
Bugu da kari kuma, za a fara aiki da filin wasa na Shekar Tsuntsaye a watan Afrilu na wannan shekara.(Tasallah)
|