Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-01-21 10:37:24    
Birnin Beijing zai hana hauhawar farashin kayayyaki da na hidima lokacin da ake gasar Olympics

cri
A ran 20 ga wata, mukaddashin magajin birnin Beijing Guo Jinlong ya bayyana cewa, birnin Beijing zai dauki matakai daban-dabam wajen ba da jagoranci kan farashin kayayyaki iri daban-dabam domin hana hauhawar farashin kayayyaki da na hidima a lokacin da ake gasar wasannin motsa jiki ta Olympics ta Beijing.

A gun taron wakilan jama'ar birnin Beijing da ake yi yanzu, Mr. Guo Jinlong ya ce, birnin Beijing zai kara mai da hankali wajen tabbatar da farashin kayayyakin masarufi da mazauna suke bukata a kullum. Kuma zai kara yin musanye-musanye da hadin guiwa da wuraren da ke samar da kayayyakin masarufi domin tabbatar da samar da kayayyakin masarufi kamar yadda ya kamata. A waje daya kuma, birnin Beijing zai dauki kwararan matakai wajen tabbatar da farashin kayayyakin masarufi.

Guo Jinlong ya kuma bayyana cewa, birnin Beijing zai kara kyautata tsarin zirga-zirga domin gasar wasannin motsa jiki ta Beijing. (Sanusi Chen)domin gasar wasannin motsa jiki ta Beijing. (Sanusi Chen)