Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-01-18 19:06:19    
Kasar Sin tana raya dimokuradiyya da tsarin dokoki daga dukkan fannoni

cri
A lokacin da ake gudanar da babban taron wakilan JKS a karo na 17 a watan Oktoba na shekarar bara, kafofin yada labaru da yawa na ketare sun mai da hankulansu kan wani abu, wato a cikin rahoton da Hu Jintao, babban sakataren kwamitin tsakiya na JKS ya bayar, ya ambaci 'dimokuradiyya' har sau 60 ko fiye, haka kuma, a matsayinta na jam'iyyar da ke mulkin kasar, JKS ta fito da dimbin sabbin tunani da bayanai bisa tushen da take tsayawa a kai a da. Sa'an nan kuma sabbin matakan da ake dauka a wurare daban daban na kasar Sin sun daukaka ci gaban raya dimokuradiyya da tsarin dokoki daga dukkan fannoni. Kafa tsari da ka'idoji kan raya dimokuradiyya da tsarin dokoki manufa ce da kasar Sin take bi.

Ran 17 ga wata, a wani kauye mai suna Dafan da ke lardin Hubei na kudancin kasar Sin, an yi jarrabawar musamman. Mazaunan wurin sun tambayi jami'an hukumar kauyensu game da batutuwan da suka mai da hankulansu a kai, kamar su kudaden da kauyensu ya samu da kuma wanda ya kashe, da zartas da kuduri kan kasa. Jami'an sun yi musu bayani filla-filla. Ban da wannan kuma, mazaunan sun ba da maki ga jami'an. Irin wannan maki ya yanke sharawa kan kudaden da wadannan jami'ai suka samu. Jiang Longping, wani jami'in kauyen Dafan ya gaya mana cewa,'A da mazaunan wurin suna iya ganin harkokin kauyensu da muka bayyana a kan bango kawai. Amma yanzu saboda an inganta kula da harkoki ta hanyar dimokuradiyya a kauyuka, mazaunan wurin sun sami damar shiga cikin harkokin kauyensu.'

Abin da ya faru a kauyen Dafan wani misali ne wajen raya dimokuradiyya a tsakanin kananan hukumomin kasar Sin. Yanzu a yankunan karkara na kasar Sin, mazaunan wuraren suna dukufa wajen tafiyar da harkokinsu da kansu ta sabbin hanyoyi.

Kauyuka na samun sauye-sauye, haka kuma, birane na samun sauye-sauye. Kazalika kuma, domin tabbatar da gudanar da ayyukan gwamnati a fili, kasar Sin ta sami kyakkyawan sakamako wajen sa kaimi kan gudanar da ayyukan gwamnati a fili har na tsawon shekaru 12. Kafa gwamnatin da ke ba da himima mai kyau shi ne makasudi na ma'aikatu daban daban na kasar Sin.

Malam Zhang Xinbao, wani shehun malami ne na kwalejin ilmin dokoki na jami'ar jama'ar kasar Sin yana ganin cewa, mayar da mutane a gaba da kome tunani ne da ake bi wajen gudanar da harkokin gwamnati a fili. Ya ce,'A zaman al'ummar kasa da ke neman gudanar da harkoki bisa doka, babbar hanyar da ake bi domin warware batutuwa da yawa ita ce gudanar da abubuwan da ke amfanawa fararen hula. Kara yin tuntuba da sassauta rikici ta hanyar bayyana harkoki a fili su ne ma'aunin da za a tabbatar da shi domin raya kasar gurguzu da ke gudanar da harkoki bisa doka, haka kuma ma'auni ne da za a tabbatar da shi domin aiwatar da ra'ayin raya kasa ta hanyar kimiyya da bunkasa zaman al'umma mai jituwa.'

Tsarawa da gyara jerin dokokin da ke da nasaba da fararen hula sosai da yin gyare-gyare kan tsarin aiwatar da doka domin kara jaddada adalci da tabbatar da ikon Bil Adama da sauran batutuwan da suka zama muhimman alamu sun nuna cewa, kasar Sin tana bin manufar kafa tsari da ka'idoji kan raya dimokuradiyya da tsarin doka.

Bugu da kari kuma, nada mutanen da ba 'yan JKS ba ne a matsayin ministocin gwamnatin ya kara fadakar da mutane da tsarin JKS game da yin hadin gwiwa da sauran jam'iyyu da ba da shawara kan harkokin siyasa. Madam Yan Junqi, shugaban kwamitin tsakiya na kungiyar sa kaimi kan dimokuradiyya ta kasar Sin ta nuna karfin zuciyarta kan tsarin jam'iyyu na kasar Sin. Ta ce,'Mun fi dora muhimmanci kan kyautata tsarin yin hadin gwiwa da kuma zurfafa nazari a fannonin shiga da ba da shawara kan harkokin siyasa. Ina da karfin zuciya saboda muna bin tsarin jam'iyyu mai sigar musamman ta kasar Sin. Bisa wannan tsari mun sami yanayin siyasa mai kwanciyar hankali da hadin gwiwa da jituwa.'

Game da dimokuradiyya mai sigar musamman ta kasar Sin, shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya ce,'Shimfida dimokuradiyya a tsakanin jama'a na da mafi muhimmanci a fannin ayyukan gurguzu. Raya harkokin siyasa na gurguzu ta hanyar dimokuradiyya makasudi ne da jam'iyyarmu ba ta canza ba, tana kuma neman tabbatar da shi.'(Tasallah)