Lallai dukannin Sinawa ba za su manta da wani mutum mai suna He Zhengliang ba. Wannan shugaba mai daukaka na kwamitin wasannin Olympic na kasar Sin bugu da kari shahararren mamban kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa ya taka muhimmiyar rawa wajen neman samun iznin shirya taron wasannin Olympic da gwamnatin Beijing ta yi har sau biyu. Tsohon babban daraktan kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa Mr. Francis Carrad ya taba fadin cewa, ya gane wa idanunsa yadda Mr. He Zhengliang ya gina wata " Babbar ganuwa" da tubali da dutse a tsanake, wadda ta cimma nasarar samun iznin shirya taron wasannin Olympics da birnin Beijing ya yi. A albarkalcin zagayowar ranar cika shekara guda da ta rage ga gudanar da taron wasannin Olympic na Beijing a shekara mai zuwa, kamar yadda dukkan Sinawa suke, kyakkyawan burin Mr. He Zhengliang zai tabbatu. Kwanan baya ba da dadewa ba, wakiliyarmu ta bakunci Mr. He don jin ta bakinsa kan kokarin da yake yi wajen bunkasa wasannin Olympic.
An haifi Mr. He Zhengliang ne a watan Disamba na shekarar 1929. Yana yin aikin wasannin motsa jiki cikin dogon lokaci. A shekarar 1981, ya zama mamban kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa; Daga baya dai, ya kama mukamin mamban zartaswa na kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa da kuma mataimakin shugaban kwamitin. Yanzu yana kan kujerar shugaban kwamitin al'adu da ilmin Olympics. Don haka, ya sami girmamawa sosai daga kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa. Irin wannan kyakkyawan tasiri da Mr. He ya yi, ya bayyanu sosai cikin jawabin da ya yi har sau biyu kan rokon neman iznin shirya taron wasannin Olympic. A lokaci daya, nasarar samun wannan izni ita ma ta cimma kyawawan mafarki da yawa na Mr. He Zhengliang. Ya furta cewa:
"Lokacin da nake yin karshen bayani kan rokon shirya taron wasannin Olympic, na fadi cewa idan kun zabi Beijing, to lallai za ku bai wa jama'a sama da biliyan guda na kasar Sin wata kyakkyawar damar yin hidimomi ga wasannin Olympics duk bisa karfinsu na kirkire-kirkire da kuma biyayyar da suke nuna wa taron wasannin Olympic".
Da Mr.He yake fadin wadannan kalmomi, mun ga wannan tsoho mai shekaru 78 a duniya yana kama da wani karamin yaro ne yake duba wakiliyarmu tare da bayyana kyakkyawar fatarsa ga dukannin Sinawa da za su cimma burinsu na gudanar da gagarumin taron wasannin Olympic bayan shekara guda.
A idon Mr. He Zhengliang, taron wasannin Olympics na Beijing, zai kasance wani gagarumin taron wasannin Olympics domin a duk tsawon yunkurin gabatar da rokon shirya taron wasannin Olympics da kuma yin share fagen taron wasannin, Sinawa sun rigaya sun gaya wa duk duniya da kuma kwamitin wasannin Olympics na kasa da kasa cewa kasar Sin wata al'umma ce dake tafiyar da harkoki cikin tsanaki". Abin da ya fi faranta ran Mr. He Zhengliang shi ne a duk tsawon wannan yunkuri, Sinawa su ma suna kokarin gyara fuskarsu sosai. Ya fadi cewa: ' Muna ta samun karin kwanancewar aiki kamar yadda ake yi tsakanin kasa da kasa. Yanzu mutane da dama dake cikin sassan da abin ya shafa kwararru ne,wadanda suka yi fice wajen aiki har suka ba takwarorinsu mamaki.
Taron wasannin Olympics na Beijing zai taimaki Mr. He Zhengliang wajen tabbatar da burinsa a fannoni da dama, wadanda suka hada da burin shiga harkar bai wa juna wutar yula ta taron wasannin Olympics na Beijing. Ya fada wa wakiliyarmu cewa : " Zan samu shekaru 79 da haihuwa a shekara mai kamawa. Labuddah zan yi alfahari da alfarma idan na samu damar rike da wutar yula mai tsarki ta Olympics".
A karshen ziyarar da wakiliyarmu ta yi wa Mr. He Zhengliang wanda ya dade har na tsawon shekaru 16 yana aiki a matsayin babban jami'in kwamitin wasannin Olympics na kasa da kasa, ya kuma fadi cewa, dukkan mambobin kwamitin su ma suna da wani kyakkyawan buri a kan cewa " babu tantama taron wasannin Olympics na Beijing zai fi kowane taron wasannin Olympics kyau da aka gudanar a da". ( Sani Wang )
|