A birnin Fuyang na lardin Anhui da ke tsakiyar kasar Sin, da akwai wasu yara wadanda iyayensu suka mutu sabo da ciwon sida, shi ya sa suka zama marayu, suna shan wahaloli da zaman kadaici sosai. Wata rana, an samo wata mace wadda take da sunan "Uwa" ga wadannan marayu, daga nan ne wadannan yara suka fara zaman jin dadi.
Wakar da kuke saurara waka ce da wata yarinya mai suna Nannan ta rera, yarinyar nan kuma tana da shekaru 16 da haihuwa. Yau da shekaru 4 da suka wuce, iyayen Nannan sun rasu daya bayan daya sabo da ciwon sida, shi ya sa ta zama wata marainiya. Abun bakin ciki sosai shi ne, Nannan ita ma ta kamu da cutar ciwon sida daga wajen uwarta.
A daidai lokacin da yarinya Nannan ta fada cikin mawuyacin zama maras mafita, ta gamu da wata malama mai suna Zhang Ying wadda take da shekaru 37 da haihuwa. Yau da shekaru 10 da 'yan kai da suka wuce, madam Zhang ta fara aikin dillancin tufafi masu suna wato shahararru da sayar da abinci da abin sha na birnin Fuyang. Sabo da madam Zhang tana da hikima da zafin nama kumatana himmar aiki, shi ya sa ta yi suna a wurin wajen yin ciniki.
Wata rana da magariba a lokacin kaka na shekarar 2003, wani al'amari ya faru ba zato wato karo na farko ne madam Zhang Ying ta gana da yarinya Nannan, a lokacin kuwa yarinyar tana tsugune ne a kasa tana jin jiki sabo da ciwonta ya tashi. Madam Zhang ta nuna jin kai sosai ga yarrinyar sabo da matsanancin halin da take ciki.
"A lokacin kuwa, ba da jimawa ba ne da na haifi jariri na zama uwa, sabo da haka ina jin cewa yarinyar nan ta yi karama har haka, kuma ta rasa iyayenta daya bayan daya, wannan ya bayar da tausayi wa mutane sosai, ga shi kuma yanzu ita kanta ma tana kamuwa da ciwon sida, ta yi rashin damar zuwa makaranta sabo da ciwon. Lalle yarinyar nan tana bukatar taimako daga sauran mutane sosai."
Kashegari, madam Zhang ta aike wa Nannan wata rigar dari ta ulu da ta auduga, kuma ta kawo mata abinci da yawa, kafin ta tashi kuma ta bar mata da kudin Sin wato Yuan 300. Amma bayan komawarta gida ta nuna damuwa sosai cewa, ramammen jikin yarinyar da kuma wahalolin da take sha yau da kullum suna jawo hankalinta. A karshe madam Zhang ta tsai da kudurin kai yarinyar birnin Beijing don ganin likita.
"Na kai mata birnin Beijing a lokacin da ya rage sauran kwanaki 4 zuwa 5 da za a yi murnar bikin bazara. Sabo da kurewar lokaci, shi ya sa bayan saukawarmu daga jirgin kasa sai mu je asibiti kai tsaye. Bayan da muka isa asibitin, na yi ayyuka da yawa kamar biyan kudin asibiti da yin gwaji da daukar hoto domin ciwon yarinyar, da sayo mata abinci, na yi ta kai da kawowa cikin asibitin."
1 2
|