Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-01-16 20:16:13    
Kiwon lafiyar jikin mata

cri

Bisa wani sabon nazari da aka yi a jami'ar Tufts ta kasar Amurka, an gano cewa, idan mata suna shan cola cikin dogon lokaci, karfin kashinsu zai samu raguwa, haka kuma za su kara samun hadarin kamuwa da cutar kashi.

Catherine Tucker da sauran manazarta na jami'ar Tufts sun gudanar da bincike kan mata 1413 da maza 1125. Daga baya kuma sun gano cewa, karfin kashin mata da su kan shan cola a ko wace rana ya kan samu raguwa idan an kwatanta shi da na wadanda ba su sha cola ko sau daya ba a cikin wata guda. Amma cola ba ta yi tasiri sosai ga karfin kashin maza ba.

Idan mata sun kamu da cutar kashi, to ksusuwansu sun fi saurin karewa, sabo da haka manazarta na kasar Australia sun ba da shawara cewa, idan tsofaffi mata suna shan magungunan ba da kariya ga lafiya da ke kunshe da sanadarin calcium a ko wace rana, to za a iya rage hadarin kamuwa da karewar kasusuwa gare su, amma muhimmin abu shi ne ya kamata a tsaya tsayin daka kan shan magungunan ba tare da kasala ba.

Mata 1460 da shekarunsu ya zarce 70 da haihuwa sun shiga nazarin. Wasu mata daga cikinsu suna shan kwayoyin calcium sau biyu a ko wace rana, kuma yawan kwayoyin calcium da suke sha a ko wane karo ya kai miligram 600, sauran mata kuwa suna shan magunguna marasa illa ga jiki domin taimaka musu wajen samun sauki. Daga baya kuma an gano cewa, shan magungunan ba da kariya ga lafiya da ke kunshe da sanadarin calcium zai ba da taimako wajen rage hadarin kamuwa da karewar kasusuwa ga tsofaffi mata.

Haka kuma manazarta sun bayyana cewa, lalle shan magungunan ba da kariya ga lafiya da ke kunshe da sanadarin calcium zai ba da taimako ga tsofaffi mata waje rage hadarin kamuwa da karewar kasusuwa, amma ana fuskantar wata matsala, wato mutane da yawa ba su iya dorewa da shan magunguna cikin dogon lokaci ba. Kusan rabi daga cikin matan da suka shiga nazarin ba su iya tsayawa kan shan magungunan da ke kunshe da sanadarin calcium ba. Kuma a cikin mata 310 da suka sha magungunan yadda ya kamata, yawansu da suka samu karewar kasusuwa ya kai kashi 10 cikin dari a cikin shekara guda, amma a cikin matan da suka sha magunguna marasa illa ga jiki domin taimaka musu wajen samun sauki, yawansu da suka samu karewar kasusuwa ya kai kashi 15 cikin dari.

To, masu sauraro, yanzu sai ku shakata kadan, daga baya kuma za mu gaya muku wani labari daban wajen kiwon lafiyar mata.

(10"??)

Ta hanyar gudanar da wani muhimmin bincike, kwararru masu ilmin aikin likita na kasar Amurka sun gano cewa, kara cin 'ya'yan itatuwa da kayayyakin lambu ga mata zai iya rage hadarin kamuwa da ciwon taruwar kitse a kan madaciya.

Manazarta na kwalejin ilmin likitanci na jimi'ar Harvard sun bayar da rahoto a cikin mujallar ilmin likitanci ta kasar Amurka, cewa mata da yawansu ya kai fiye da dubu 77 sun shiga wannan bincike mai suna "nazari kan kare lafiyar jiki" wanda za a gudanar da shi cikin dogon lokaci. Daga baya kuma sakamakon ya bayyana cewa, mata 6600 sun kamu da ciwon taruwar kitse a kan madaciya lokacin da ake gudanar da wannan bincike cikin shekaru 16, kuma an yi musu tiyatar cire madaciya. Ban da wannan kuma an bayyana cewa, yiyuwar kamuwa da ciwon taruwar kitse a kan madaciya ga mata wadanda suke cin 'ya'yan itatuwa da kayayyakin lambu mafi yawa ya ragu da kashi 21 cikin dari idan an kwatanta ita da wadanda suka ci 'ya'yan itatuwa da kayayyakin lambu dan kadan.

Ban da wannan kuma manazarta sun yi hasashen cewa, kara cin 'ya'yan itatuwa da kayayyakin lambu musamman ma kayayyakin lambu da ke da koren ganyaye da 'ya'yan itatuwa kamar lemo da kuma sauran abincin da ke kunshe da bitamin C da yawa zai ba da taimako wajen magance taruwar kitse a kan madaciya. Kuma game da wadanda suka kamu da ciwon, yin haka zai taimake su wajen hana tsanantar ciwon.

To, jama'a masu sauraro, shirinmu na yau na ilmin zaman rayuwa ke nan. Muna fatan kun ji dadinsu, da haka Kande ce ke shirya muku wannan shiri kuma ke cewa mako gobe war haka idan Allah ya kai mu.(Kande Gao)