Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-01-16 20:12:09    
Wani daraktan sinima na kasar Sin

cri

Xiao Feng yana da shekaru 49 da haihuwa a wannan shekara, yana daya daga cikin fitattun daraktocin sinima na kasar Sin.

Tun lokacin da yake karami, Xiao Feng yana matukar sha'awar zane-zane da sinima. Amma a shekarun 1960, ba a samu ingantaccen zaman rayuwar jama'a ba a kasar Sin. A lokacin, abin kece raini ne ga wani yaro da ya je kallon sinima. Xiao Feng ya ce, " A lokacin, mutanen da na fi kyashi su ne masu zana takardun tallan sinima da za a nuna a gidan sinima. A ganina, su mutane ne da suke iya kallon sinima ko wace rana. Sabo da babu yadda za su yi su iya zanen nan ba, sai dai sun sami labarin da aka bayar a cikin sinima sosai. Shi ya sa na kan ga takardar tallan sinima da farko, idan zanen da aka yi ya yi kyau, to, zan je kallon sinima din. Na girmama mutanen da suke zanen takardun tallan sinima sosai."

Xiao Feng ya ci gaba da cewa, don neman kallon sinima, ya kan kwaikwayi zanen da aka yi a kan tikitin sinima bisa baiwar da Allah ya ba shi wajen fasaha, har ma ya kai ga ba a iya bambanta tikitin da ya kwaikwaya da tikiti na gaskiya.

Xiao Feng ya tuna da sinima ta farko da ya gani mai suna "Bayi", inda aka bayar da labarin zaman rayuwar bayi kafin a yantar da Tibet cikin lumana, wannan sinima ya kawo masa babban tasiri. Ya ce,"bayan da na ga sinima din, ban yi barci ba a duk dare. Ban san ana iya samun mutane masu ban tausayi haka ba a duniya. Wannan sinima ya kawo babban tasiri a kan rayuwata da ra'ayoyina. Shi ya sa irin halin ayyukan da na yi daga baya ya dogara sosai ga wannan sinima da na gani tun da nake karami."

A shekarar 1980, Xiao Feng ya gama karatunsa a jami'ar koyon aikin fasaha ta birnin Nanjing, kuma ya zama wani mai zanen sinima. A ganinsa, ya matso kusa da burinsa. Sabo da kyakkyawan sakamakon da ya samu wajen yin aikinsa, an ciyar da shi gaba don ya zama wani dan zane mai zaman kansa lokacin da yake da shekaru 24 da haihuwa kawai. Xiao Feng ya ce, "Mene ne burina a lokacin? Burina shi ne in zama wani daraktan sinima. Daga karshe, bayan da na yi shekaru 7 ina wannan aiki na mai zane, na yi sinimomi 7. A lokacin, na sha wahala, amma ina son aikina sosai. Amma duk da haka, kullum ina tunanin yadda sauran daraktocin sinima suke aiki. Ya zuwa shekarar 1987, ban ci gaba da gamsuwa da zama wani mai zane ba. Ina ganin na karu, ya kamata in zama wani daraktan sinima."

Don neman cimma burinsa, a shekarar 1991, Xiao Feng ya fara karatu a sashen koyon aikin daraktan sinima na jami'ar koyon ilmin sinima ta Beijing. Ya kago labaru da kansa, ya kuma nemi 'yan kasuwa da su zuba jari, har ya fitar da wasu wasannin kwaikwayo na telebiji, amma ainihin burinsa shi ne yin sinima.

Sinima mai suna "Zo! Fada da kafarka" sinima ta farko ce da aka dauka a jagorancinsa. Wannan sinima ta bayar da labarin 'yan wasan kwallon kafa biyu na kasar Sin wadanda ke kokarin neman ciyar da sha'anin wasan kwallon kafa na kasar Sin gaba. Daga baya, ya yi wasu sinima na yara a jere, har ma sau da yawa ne ya sami lambar yabo ta "saniyar tagulla", wato lambar yabo ta koli da aka baiwa kyakkyawan sinima na yara a kasar Sin.

Ban da sinima, Xiao Feng ya kuma ba da jagoranci a kan wasannin kwaikwayon telebijin da dama wadanda suka sami martani mai kyau sosai daga wajen 'yan kallo. A cikin wasannin telebijin mai suna "zamanin jarumai" da aka nuna ba da dadewa ba, an bayyana takarar ciniki da ake yi tsakanin masana'antun gwamnati da na masu zaman kansu a zamanin yanzu, inda kuma aka nuna sabanin ra'ayoyi mai tsanani tsakanin mutanen bangarori daban daban na kasar Sin, ban da wannan, an kuma bayyana fahimtar mutanen bangarori daban daban game da rayuwa da soyayya da kuma kudi. Wasannin telebijin din sun sami yabo sosai musamman domin ya tabo irin ra'ayin nuna damuwa ko a cikin halin zaman lafiya da jam'iyyar da ke jan ragamar mulki ta kasar Sin ta nuna.