Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-01-16 07:51:16    
Kungiyar Olympic ta kasar Sin tana yin kokari domin samun sakamako mai gamsarwa a gun gasar wasannin Olympic ta Beijing

cri

Kamar yadda kuka sani,a kullum wasan kwallon kafa na maza ya fi jawo hankulan `yan kallon gasar wasannin Olympic,saboda haka,domin samun sakamako mai gamsarwa a gun gasar wasannin Olympic ta Beijing,kungiyar wasan kwallon kafa ta kasar Sin ta kafa kungiyar wasan kwallon kafa ta Olympic ta kasar Sin.A tsakiyar watan Disamba na shekarar 2007,bi da bi ne kungiyar Olympic ta kasar Sin ta yi gasar sada zumunta da kungiyar Olympic ta kasar Amurka da kungiyar Cottbus ta kasar Jamus sau uku a birnin Changsha da birnin Guangzhou da kuma birnin Fushan dake kudancin kasar Sin.Bayan gasar da suka yi,matsayin kungiyar Olympic ta kasar Sin ya dada daguwa a bayyane,ta hakake cewa,za ta samu sakamako mai kyau a gun gasar wasannin Olympic ta Beijing.

A tsakiyar watan Disamba na shekarar da ta wuce,kungiyar Olympic ta kasar Sin da kungiyar Olympic ta kasar Amurka sun yi gasa sau biyu,kuma sun yi kunnen doki.A gun gasar dake tsakaninta da kungiyar Cottbus ta kasar Jamus wadda ke da karfi sosai,kungiyar Olympic ta kasar Sin ta yi kokari,a karshe dai su ma sun yi kunnen doki.Game da wannan,babban malamin koyar da wasa na kungiyar Olympic ta kasar Sin wanda shi ne `dan asalin kasar Serbia Ratomir Dujkovic ya darajanta kungiyar sosai.Ya ce:  `Lallai kungiyarmu ta kasa jefa kwallo cikin raga a mataki na karshe,amma `yan wasanmu za su sami ci gaba saboda suna sanya matukar kokari a ko da yaushe.`

Domin yin takara da kungiyoyi daban daban a nan gaba,kungiyar Olympic ta kasar Sin ta yi gwaji da fasahar gasa iri daban daban yayin da take yin gasar sada zumunta.Alal misali,a gun gasar dake tsakaninta da kungiyar Olympic ta kasar Amurka,babban malamin wasa Dujkovic ya yi gwaji da wata sabuwar fasaha wadda bai taba yin amfani da ita ba a da.Mai tsaron gaba na kungiyar Zhu Ting ya gaya mana cewa,  `Kodayake yanzu ba mu saba da sabuwar fasaha ba,amma halin da muke ciki zai sami kyautatuwa a nan gaba.`

`Yan wasan kungiyar Olympic ta kasar Sin suna ganin cewa,makasudin shiga gasar sada zumunta shi ne domin yin bincike kan sakamakon atisayen da aka samu,daga baya kuma za a tarar da matsala dake gabansu,a karshe dai za a daga matsayi.Ana iya cewa,yanzu an riga an cimma burin da suka kimanta.

Yayin da yake takalo magana kan wane ne zai samu iznin shiga gasar wasannin Olympic ta Beijing,babban malamin wasa Dujkovic ya ce,  `A ganina,yawancin `yan wasan kungiyar Olympic ta kasar Sin za su shiga gasar wasannin Olympic ta Beijing,amma yanzu lokaci bai yi ba da mu sanar da hakikanan sunayen `yan wasa,duk da haka,ko shakka babu,dukkan `yan wasan kungiyar Olympic ta kasar Sin za su sami ci gaba bayan kokarin da suke yi.`

A cikin shekarar da ta wuce,wato shekarar 2007,kungiyar Olympic ta kasar Sin ta sha aiki sosai da sosai,wato `yan wasan kungiyar sun taba zuwa Turai sau uku kuma sun taba zuwa Afirka sau daya domin yin atisaye,kuma sun taba shiga gasa sau tarin yawa a can.A gun gasar dake tsakaninta da sauran kungiyoyin `yan wasan kwallon kafa na kasashe daban daban,kungiyar Olympic ta kasar Sin ta samu sakamako mai kyau,dalilin da ya sa haka shi ne domin a kullum tana yin aikin share fage sosai da sosai.

Babban malamin wasa Dujkovic ya gamsar da sakamakon da kungiyar Olympic ta kasar Sin ta samu a cikin shekarar 2007 sosai,ya ce,a takaice dai,ana iya cewa,sun riga sun sami cikakkiyar nasara.A shekarar bana kuwa,za su ci gaba da sanya matukar kokari,suna fatan za su samu sakamako mai kyau a gun gasar wasannin Olympic ta Beijing.(Jamila Zhou)