Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-01-16 07:49:26    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki (09/01-15/01)

cri

Ran 11 ga wata,agogon wurin,a birnin Lausanne na kasar Switzerland,wani jami`in babbar kungiyar wasan sukuwar dawaki ta kasashen duniya ya darajanta aikin share fage da yankin musamman na kasar Sin Hongkong ke yi domin shirya gasar sukuwar dawaki ta gasar wasannin Olympic ta shekarar 2008 sosai da sosai,kuma ya bayyana cewa,babbar kungiyar wasan sukuwar dawaki ta kasashen duniya ta tabbata cewa,Hongkong kasar Sin zai shirya gasar sukuwar dawaki ta gasar wasannin Olympic lami lafiya.Babbar kungiyar wasan sukuwar dawaki ta kasashen duniya tana ganin cewa,Hongkong na kasar Sin yana kokarin shirya gasar sukuwar dawaki ta gasar wasannin Olympic,kuma ya gina gine-ginen da abin ya shafa iri? na zamani,musamman wajen aikin kare dawakin gasa,masu aikin shirya gasar suna sanya matukar kokari domin samar da aikin hidima mai kyau ga dawakin gasa,shi ya sa babbar kungiyar wasan sukuwar dawaki ta dauka cewa,Hongkong zai shirya gasar lami lafiya.Babbar kungiyar ta fayyace cewa,za ta shirya wani taron share fagen da ake kiransa da suna `dosa gaba zuwa Hongkong` a birnin Lausanne a watan Fabrairu na bana,inda za a yi bayani ga mambobin kungiyar kan matakai daban daban da Hongkong ke dauka domin gasar sukuwar dawaki ta gasar wasannin Olympic ta Beijing.

Ran 11 ga wata,agogon wurin,a gun zagaye na karshe na gasar dake tsakanin mata biyu biyu ta gasar wasan tennis ta duniya da ake yi a birnin Sydney na kasar Australia,`yan wasa daga kasar Sin Zheng Jie da Yan Zi sun lashe `yar wasa daga kasar Belarus Tatiana Poutchek da `yar wasa daga kasar Ukrain Tatiana Perebiynis wadanda suka yi hadin gwiwa tsakaninsu,kuma suka samu zama na farko.Daga baya kuma za su shiga budaddiyar gasar wasan tennis ta kasar Australia.

Ran 14 ga wata da asuba,agogon Beijing,aka kammala gasar cin kofin duniya ta wasan kankara ta samari ta duniya ta shekarar 2008 a kasar Italiya.A gun gasar ba da sanda ta maza ta mita dubu biyu da aka shirya a rana ta karshe,kungiyar kasar Sin ta samu zama na uku,wato kungiyar kasar Korea ta kudu ta samu zama na farko,kuma kungiyar kasar Faransa ta samu zama na biyu a bayanta.

Ran 13 ga wata da asuba,agogon Beijing,aka yi zagaye na 27 na hadaddiyar gasar zakarun wasan kwallon kafa ta Ingila ta wannan shekarar gasa,kungiyar Charlton ta lashe kungiyar Blackpool cikin sauki,`dan wasa daga kasar Sin na kungiyar Charlton Zheng Zhi ya jefa kwallo biyu cikin raga. (Jamila Zhou)