Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-01-15 21:23:21    
Kasar Sin ta ki yarda da yunkurin sanya siyasa cikin gasar wasannin Olympic

cri
Ran 15 ga wata, a nan Beijing, a gun taron manema labaru da aka saba shiryawa, madam Jiang Yu, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin ta bayyana cewa, kasar Sin ta ki yarda da dukkan yunkurin sanya siyasa cikin gasar wasannin Olympic.

A lokacin da take amsa tambayoyin da manema labaru suka yi mata, madam Jiang ta ce, gasar wasannin Olympic kasaitaccen biki ne ga dukkan jama'ar kasa da kasa. Haka kuma samun nasarar shirya gasar wasannin Olympic buri ne na dukkan jama'ar kasashen duniya. Gwamnatin Sin tana himmantuwa wajen share fagen gasar wasannin Olympic daga dukkan fannoni. A irin wannan lokaci, domin wasu boyayyun makasudan siyasa ne wasu kungiyoyi suka bullo domin tallata wasu batutuwa, sun hada su da gasar wasannin Olympic tare domin neman bata kyakkyawar siffar kasar Sin da kuma matsa wa gwamnatin Sin lamba. A bayyane ne abin da suka yi ya saba wa ra'ayin wasannin Olympic da ka'idojin wasannin Olympic, shi ya sa tabbas ne za su ci tura.

Bugu da kari kuma, wannan kakaki ta kara da cewa, a kan batun hakkin dan Adam, har kullum kasar Sin tana tsayawa tsayin daka kan ganin ya kamata kasashen duniya su rage sabani a tsakaninsu ta hanyoyin yin mu'amala da tattaunawa da kuma hadin gwiwa bisa tushen girmamawa juna da yin zaman daidai wa daida, ta haka za su daukaka ci gaban aikin kiyaye hakkin dan Adam na duniya tare.(Tasallah)