In an tabo magana kan filin wasa na ma'aikata da kuma dakin wasa na ma'aikata a nan Beijing, babu tantama babu wanda bai san su ba. A matsayin gine-gine 2 da suka zama alamar Beijing a shekaru 60 na karni na 20, an taba yin dimbin gasanni da wasannin kwaikwayo da ba a iya kidaya yawansu ba a wajen, mutane da yawa suna farin ciki tuna baya. Bayan da muka shiga cikin sabon karni, ana yin kwaskwarima ga wadannan gine-gine 2 masu tsawon shekaru kusan 50, wadanda za a yi shirye-shiryen wasan kwallon kafa da na dambe na gasar wasannin Olympic ta Beijing ta shekarar 2008. Nan gaba ba da jimawa ba, wadannan gine-gine 2 za su bayyana ga mutane cikin wata sabuwar siffa. Yau ma bari in yi muku bayani kan filin wasa na ma'aikata na Beijing.
Za a yi shirin wasan kwallon kafa a filin wasa na ma'aikata na Beijing a lokacin da ake yin gasar wasannin Olympic ta Beijing. An kammala gina wannan filin wasa a ran 31 ga watan Agusta na shekarar 1959, yana kuma daya daga cikin manyan gine-gine 10 da suka shahara a Beijing a lokacin da ake murnar cikon shekaru 10 da kafuwar sabuwar kasar Sin. Yawan 'yan kallo da wannan filin wasa ya iya karba bai kai dubu 80 ba.
An fara yin kwaskwarima da kuma fadada filin wasa na ma'aikata na Beijing a ran 18 ga watan Afrilu na shekarar 2006. An inganta tsarin ginin filin wasan da kyautata filin ciyayi na gasa da kuma hanyoyin tsere na simintin roba domin biyan bukatun da kwamitin wasan Olympic na kasa da kasa da hadaddiyar kungiyar wasan kwallon kafa ta kasa da kasa da kuma kwamitin shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing suka gabatar. A ciki ayyukan kwaskwarima da yawa da aka yi wa wannan filin wasa, filin ciyayi ya fi jawo hankulan mutane. An shimfida wayar samar da zafi daga wutar lantarki a karkashin filin ciyayin. A ko wace shekara an samar wa ciyayi zafi domin ganin su sake zama kore kafin lokaci ya yi, an yi iyakacin kokari domin samun isasshen lokaci a fannin adana ciyayi yadda ya kamata. Yanzu an kammala yin kwaskwarima kan filin ciyayin. An yi karin bayani cewa, a shekarar 2008, filin ciyayi da ke cikin filin wasa na ma'aikata na Beijing zai yi daidai da na filin wasan kwallon kafa na Wembley na kasar Birtaniya.
Yin gyare-gyare kan filin ciyayi na filin wasa na ma'aikata na Beijing ya yi kama da bai wa wani tsoho wata zuciya mai karfi. Yanzu in ka sake shiga wannan filin wasa, za ka gano wani sabon filin wasa na ma'aikata. A cibiyarsa, akwai filin wasan kwallon kafa, wanda aka rufe shi da ciyayi, sa'an nan kuma, jan hanyoyin tsere guda 8 masu tsawon 400 suna kewayensa. Ban da wannan kuma, an samar wa 'yan kallo kujeru masu launuka 5 a bangarori 4 na filin wasan. A kan kujerun 'yan kallo kuwa, aka fito da wata babbar rumfa tare da fitilu fiye da 300. In an yi gasa da dare a wajen, bayan da aka kunna dukkan fitilu, sai ka ce rana ya sake fitowa. Kazalika kuma, an rataya injunan sitiriyo a karkashin wannan babbar rumfa, an iya jin karar da ke fitowa daga wannan injuna tangaran. A kudancin filin wasan, an ajiye allon nune-nune na lantarki mafi girma a Asiya, wanda ya iya nuna takara mai tsanani a filin wasan daga bangarori daban daban.
|