Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-01-15 15:51:25    
Jami'a ta farko da kasar Sin da kasashen waje suka kafa kuma ake gudanarwa tare a nan kasar Sin

cri

Assalam alaikum, jama'a masu sauraronmu, barkanku da war haka, barkanmu da sake saduwa a cikin shirinmu na yau na kimiyya da fasaha da kuma ilimi. A cikin shirinmu na yau, za mu yi muku wani bayani game da jami'ar Norttingham ta Ningbo, wato jami'a ta farko da kasar Sin da kasashen waje suka kafa kuma ake gudanarwa tare a nan kasar Sin. To, masu sauraro, yanzu ga cikakken bayani.

A birnin Ningbo na jihar Zhejiang da ke gabashin kasar Sin, akwai wata jami'ar da ke da muhalli mai kyau, ita ce kuma jami'a ta farko da kasar Sin da kasashen waje suka kafa kuma ake gudanarwa tare, wadda ma'aikatar ba da ilmi ta kasar Sin ta amince da ita. Mr. Roger Woods, mataimakin shugaban jami'ar, da kuma malamai kusan 140 daga wurare daban daban na dukkan duniya suna aiwatar da tsarin ba da ilmi na duniya.

Mr. Woods ya zo kasar Sin ne daga birnin Nottinham da ke tsakiyar kasar Burtaniya, don dare kujerar mataimakin shugaban jami'ar Nottingham ta Ningbo. "Ko shakka babu, ina son aiki a kasar Sin. Sabo da wannan kasa ce mai karfi, kuma tana dacewa da halin makarantarmu. Muna da dama da yawa a nan."

Bayan da Mr. Woods ya zo kasar Sin, a matsayinsa na wani mataimakin shugaban jami'ar Nottingham, aikin da ya fi muhimmanci a gabansa shi ne, kafa wata kungiyar malamai mai inganci ga jami'ar. Amma, a farko bai iya tabbatar da mutane nawa ne za su nemi aikin malanta a jami'arsu ba. "Saboda muna gudanar da wani sabon tsarin kafa makaranta, har ma ba mu iya hasashe ko mutane za su nuna sha'awa kan wannan ba. Amma, mun sadu da roko daga kwararru masu inganci a dukkan duniya, lallai mutane da yawa sun nuna sha'awa ga kasar Sin, kuma suna son aiki a kasar Sin. A karshe dai mun samu malamai masu inganci sosai daga cikinsu."

Mr. Woods ya gabatar da cewa, yanzu akwai malamai kusan 140 a jami'arsu, yawancinsu sun zo daga kasashen Burtaniya, da Australia, da Amurka, da Canada, da Malaysia, da dai sauransu. Wadannan malamai suna aiki da zama a birnin Ningbo, har ma wasu daga cikinsu sun dawo da iyalinsu a birnin. Ma'aikatan jami'ar na bangaren Sin kuma suna kula da ayyukan harkokin zaman yau da kullum, da ba da guzuri, da kuma yin cudanya, da dai sauransu, ba su shiga aikin ba da ilmi, kuma ba su yin kafar ungulu ga dabarun koyarwa na ma'aikatan bangaren ketare. Mr. Woods ya sha buga take yayin da yake tabo magana kan takwarorin aikinsa, cewa,. "Abokan aikinmu na kasar Sin suna nuna goyon baya sosai ga aikinmu, sun taimake mu a fannoni da yawa. Lallai ake iya cewa, idan babu taimakonsu, to, ba za mu iya kafa makarantarmu ba."

Mr. Woods ya kan ba da darussa shi da kansa a jami'ar, inda har kullum yake kokarin fadakar da dalibai na kasar Sin da irin tunanin kasar Burtaniya. Hakan ya gano bambancin da ke tsakaninsu da kuma na kasarsa. Mr. Woods ya yi yabo sosai ga dalibai na kasar Sin a kan cewa, "A ganina, daliban kasar Sin suna bayyana ra'ayoyinsu kai tsaye, amma a kasar Burtaniya, mutane su kan yi hankali kan wannan. Ina son hanyar bayyana ra'ayoyi ta daliban kasar Sin, saboda ta haka na iya sanin abubuwan da dalibanmu ke bukata. Bayan haka kuma, daliban kasar Sin suna yin kokari sosai kan karatu, suna iya samun ilmi da sauri."

Ban da daliban kasar Sin kuma, a jami'ar Nottinham akwai dalibai daga kasashen waje. Mr. Woods ya gaya mana cewa, yana fatan ba da dama da yawa ga wadannan dalibai na Sin da na ketare, domin sanin duniya. Yanzu yana kokari kan jawo daliban kasashen waje da yawa zuwa jami'ar Nottingham, don yin karatu, da kuma sanya daliban kasar Sin fita waje don samun ilmi.