Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-01-14 16:38:27    
wasu labaru game da kananan kabilun kasar Sin

cri

A karshen shekarar 2007, manoma masu yaki da talauci na jihar Tibet ta kasar Sin sun samu kudin taimako bisa ma'aunin zaman rayuwa mafi kankanta a karo na farko bayan da aka fara gudanar da tsarin samar da kudin taimako a kauyukan jihar. Yanzu lokacin hutun aikin gona ya yi da manoma da makiyaya na jihar Tibet suke fuskantar yanayin sanyi, sabo da haka wannan kudin taimakon da aka bayar ya tabbatar da cimma daidaito kan wahalolin zaman yau da kullum ga jama'a masu yaki da kangin talauci.

Gundumar Jiangzi da ke shiyyar Shigatse wata shiyya ce da aka samar da kudin taimako bisa ma'aunin zaman rayuwa mafi kankanta a kauyukan jihar Tibet tun da wuri. A ran 12 ga wata, ma'aikatan hukuma na sassan kula da harkokin jama'a sun ba da kudin taimako ga mutane 125 masu yaki da talauci.

---- A gun taron ayyukan tattalin arzikin duk jihar Tibet da aka yi kwanan baya a birnin Lhasa, Mr. Zhang Qingli, sakataren kwamitin jam'iyya na jihar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta ta kasar Sin ya nanata cewa, jihar Tibet za ta sa aikin kyautata sharudan aikin kawo albarka da na zaman yau da kulla na manoma da makiyaya, da kara samar musu da kudin shiga bisa matsayin farko domin bunkasa tattalin arziki da zaman al'umma.

A gun wannan taro kuma, jihar Tibet ta dauki manyan alkawara 3 ga manoma da makiyaya, wato na farko zuwa shekarar 2010, za a zaunar da manama da makiyaya da yawansu ya wuce kashi 80 cikin 100 bisa na dukkan jihar cikin gidaje masu kyau. Na 2, za a shimfida bututun ruwan sha da hanyoyin watar lantarki da hanyoyin mota da rediyo da telebijin da sadarwa zuwa kauyuka daban-daban na duk jihar. Na 3, za a kafa kwamitin kauye da dakunan wasanni a dukkan kauyukan jihar. An kimanta cewa, matsakaicin yawan kudin shiga da kowane manomi da makiyayi zai samu a shekara mai zuwa zai zarce kudin Sin wato Yuan 3,000.

---- A shekarar 2008, jihar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta ta kasar Sin za ta ware kudin Sin wato Yuan miliya 24 domin ayyukan samar da sabbin makamashi, ta yadda manoma da makiyaya mafi yawa za su iya yin amfani da makamashin hasken rana da na halittu masu rai da sauran makamashin bola jari wato makamashin da za a iya sake samu kullum maimakon kiraren da suke yin amfani da shi yau da kullum.

Tun dogon lokacin da ya wuce, jama'a 'yan birane da na garuruwa na jihar Tibet musamman ma manoma da makiyaya wadanda suka mai da itatuwa da kashin shanu da na tumaki a matsayin muhimman abubuwan konawa cikin zaman yau da kullum, sabo da haka ana lalatawa tare da rage bishiyoyin jihar Tibet, wannan yana kawo mummunan tasiri ga muhallin halittu masu rai na jihar. Gwamnatin jihar ta yi hankoron samun makamashin hasken rana da na halittu masu rai da na zafin karkashin kasa da sauran makamashi masu tsabta cikin shekaru 10 masu zuwa, don haka an rage yawan dogaro da jama'a ke yi bisa makamashin kiraren da suke amfani da shi kullum.