Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-01-14 16:34:47    
Kasar Sin tana kokari wajen bunkasa aikin haka ma'adinai ba tare da gurbata muhalli

cri

Albarkatun ma'adinai muhimman kayayyaki ne da ake amfani da su wajen bunkasa zamantakewar al'umma a duniya. A sakamakon ci gaba da ake samu wajen bunkasa harkokin tattalin arziki cikin sauri, yawan ma'adinai da ake bukata kullum sai kara karuwa yake yi, sa'an nan kuma ana kara gurbata muhalli, yayin da ake bunkasa aikin haka ma'adinai.

A kwanakin baya, a birnin Beijing, an bude taron kasa da kasa kan aikin haka ma'adinai na kasar Sin a karo na 9. Jami'an hukumomi da kwararru da masanan ilmin kudi da ciniki da kimiyya da fasaha sama da 2000 wadanda suka fito daga kasashe da shiyyoyi sama da 30 sun halarci taron. Inda suka tattauna a kan babbar manufa game da raya kasa ta hanyar kimiyya da sa kaimi ga bunkasa aikin haka ma'adinai ba tare da gurbata muhalli ba. Malam Xu Shaoshi, mininstan filayen kasa da albarkatu na kasar Sin ya bayyana a gun taron cewa, kasar Sin za ta gaggauta bunkasa aikin haka ma'adinai ba tare da gurbata muhalli ba. Ya ce, "a sakamakon ci gaban da ake samu wajen bunkasa aikin haka ma'adinai cikin sauri, gwamnatocin kasashe daban daban da masana'antu da bangarorin jama'a daban daban na kasa da kasa suna kara mai da hankali ga yin amfani da albarkatun kasa yadda ya kamata da kiyaye muhalli da sauran manyan batutuwa. Gaggauta bunkasa aikin haka ma'adinai ba tare da gurbata muhalli ba yana kara zama ra'ayi daya ga jama'a. Yanzu, kasar Sin na kokari sosai wajen aiwatar da babbar manufarta game da samun bunkasuwa ta hanyar kimiyya da tsimin makamashi da kiyaye muhalli."

Kungiyar hadin kan masu aikin haka ma'adinai ta kasar Sin wata kungiya ce dake kunshe da masu aikin haka ma'adinai iri daban daban. Makasudinta shi ne sa kaimi ga bunkasa aikin haka ma'adinia. Malam Li Yuan, shugaban kungiyar ya ce, kungiyarsa tana taka muhimmiyar rawa wajen sa kaimi ga bunkasa aikin haka ma'adinai ba tare da gurbata muhalli ba. Ya kara da cewa, "a cikin shekarun nan, mun kara kokari wajen yin bincike kan manyan batutuwa, mun gabatar wa gwamnati sakamakon bincike da muka samu kamar "ma'auni mafi karanci kan aikin haka ma'adinai masu muhimmanci da ire-irensu", da "tsarin ma'aunin tattalin arzikin bola-jari a fannin albarkatun kasa", kuma mun rubuta bayanonin koyarwa a kan tsimin albarkatun ma'adinai da kara yin amfani da su a fannoni daban daban."

Babban kamfanin haka kwal na Datong na jihar Shanxi da ke a tsakiyar kasar Sin yana daya daga cikin sansanonin haka kwal mafi girma a kasar Sin. Yawan kwal da yake hakowa ya kai kimanin tan miliyan 100 a ko wace shekara. A watan Yuli na shekarar bara, kamfanin ya kafa wani yankin haka ma'adinai na zamani da ake kira Tashan, wanda ya riga ya gwada kyakkyawan misali ga aikin haka ma'adinai ba tare da gurbata muhalli ba. Don haka ya jawo hankulan bangaren masu aikin haka ma'adinai na kasar Sin sosai.

Bisa kokarin da ta yi wajen bunkasa aikin haka ma'adinai ba tare da gurbata muhalli ba, kasar Sin ta sami amincewa da yabo daga wajen bangarorin haka ma'adinai na duniya. Malam William Bulmer, babban darektan hukumar zuba jari kan aikin ma'adinai ta kamfanin aikin kudi na duniya wadda bankin duniya ke mallaka ya bayyana cewa, "bankin duniya ya yi farin ciki sosai da ganin yadda gwamnatin kasar Sin da kamfanonin haka ma'adinai da hukumomin kula da aikin haka ma'adinai na kasar Sin suka dauki kyawawan matakai, don ba da tabbaci ga kiyaye muhalli yayin da ake haka ma'adinai a kasar Sin da sauran kasashe. Mun hakake, kamfanonin haka ma'adinai za su iya kara taka muhimmiyar rawa wajen aiwatar da manufar kamfanin aikin kudi na duniya game da samun bunkasuwa mai dorewa, kuma za su iya gwada kyakkyawan misali ga bunkasa aikin haka ma'adinai cikin dogon lokaci."

(Halilu)