Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-01-12 20:31:34    
Ana gudanar da ayyukan tsaro daban daban na wasannin Olympic na Beijing kamar yadda ya kamata

cri
Yau 12 ga wata, shugaban hukumar tsaron jama'a na birnin Beijing Ma Zhengchuan ya bayyana a nan birnin Beijing cewa, yanzu ana gudanar da ayyukan tsaro daban daban na wasannin Olympic kamar yadda ya kamata.

Mr. Ma Zhengchuan ya gabatar da cewa, birnin Beijing, da hukumomin da abin ya shafa na kasar sun riga sun tsara hakikanin shirin tsaro na wasannin Olympic, kuma sun kafa tsarin jagoranci na aikin tsaro na wasannin Olympic, kazalika sun tsara shirin kuduri fiye da 540. A waje daya kuma, kan halin yaki da ta'addanci da kasashen duniya ke ciki, birnin Beijing ya kafa hukumar jagoranci don magance yaki da ta'addanci na gaggawa, bugu da kari kuma, bangaren 'yan sanda ya tattara kwararrunsa, da kuma kafa tsarin fasaha da na'u'rorin da suka fi zama na zamani a duniya, hakan kuma an kara karfin sarrafa wuraren jama'a, da na magance ayyukan ta'addanci.

Bayan haka kuma, tun daga shekarar 2003, sau da yawa bangaren 'yan sanda na birnin Beijing ya aika da 'yan sanda zuwa birnin Athens, da birnin Sydney, da kuma sauran biranen da suka taba shirya wasannin Olympic, don koyon fasahohin tsaro na wasannin Olympic. (Bilkisu)