Yau a nan birnin Beijing, shugaban hukumar kula da yanayi ta kasar Sin, Mr.Zheng Guoguang ya bayyana cewa, yanzu sassan kula da yanayi na kasar Sin a shirye suke za su samar da bayanan yanayi mafi inganci ga wasannin Olympics da za a gudanar a birnin Beijing.
Mr.Zheng Guoguang ya ce, tun bayan da birnin Beijing ya fara karbar bakuncin gudanar da wasannin Olympics, kullum sassan kula da yanayi na kasar Sin suna share fage daga dukan fannoni, ciki har da kara raya tsarin sa ido kan yanayi a birnin Beijing da dai sauran biranen da za su hada kansu da Beijing wajen gudanar da wasannin, da hada gwiwa da gamayyar kasa da kasa don daidaita matsalolin fasaha a fannin hasashen yanayi a lokacin gudanar da wasannin Olympics, da kimanta bala'i daga indallahi da mai yiwuwa za a gamu a lokacin wasannin Olympics, da kuma gudanar da gwaje-gwajen bayanan yanayi da sauransu.(Lubabatu)
|