Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-01-11 15:34:51    
Dakin karatu na kasar Sin

cri

Tambayar da za mu amsa a wannan mako ta fito ne daga hannun Ilyasu Bawa Karshi da malam Ahmad Jagaba Karshi, mazaunan Garki Abuja, tarayyar Nijeriya. A cikin wasikar da malaman suka rubuto mana, sun ce, suna son a ba su tarihin dakin karatu mafi girma a kasar Sin. Sabo da haka, a cikin shirinmu na yau, bari mu dan gutsura muku tarihin babban dakin karatu na kasar Sin.

Dakin karatu na kasar Sin asalinsa shi ne dakin karatu na Jingshi. A farkon karni na 20, a yayin da ake kokarin gyare-gyare don neman kara karfin kasa da koyon fasahohin kasashen yammacin duniya a nan kasar Sin, wasu masu hangen nesa sun yi kokarin shawartar gwamnatin daukar Qing da ta kafa dakin karatu, don inganta al'adun al'ummar da kuma shigowa da ilmin kimiyya na zamani. Sabo da haka, a shekarar 1909, sarki Xuantong ya amince da kafa dakin karatu na Jingshi. A shekarar 1929, an kuma hade shi da dakin karatu na Beihai. Daga baya, a shekarar 1931, aka gama kafa sabbin harabobinsa a titin Wenjin. Sabo da haka, ya zama dakin karatu da ya fi girma da kuma samun cigaba a kasar Sin a wancan lokaci. Bayan da aka kafa jamhuriyar jama'ar Sin, sakamakon bunkasuwar kasa da kuma karuwar bukatun jama'a a fannin al'adu, ko da yake an yi ta habaka wannan dakin karatu, amma duk da haka, ba a cimma biyan bukarun jama'a ba. Sabo da haka kuma, a shekarar 1975, marigayi Zhou Enlai, wanda ya kasance firaminista na farko na jamhuriyar jama'ar Sin, ya ba da shawarar gina sabbin harabobin dakin karatu na Beijing, an kuma kammala wannan aiki a shekarar 1987. A shekarar 1998 kuma, aka sake sunan wannan dakin karatu zuwa dakin karatu na kasar Sin.

Littattafai iri iri masu yawan gaske ne da ke akwai a cikin dakin karatu na kasar Sin, ciki har da na zamanin da da na yanzu da na gida da na waje. Ya zuwa karshen shekarar 2003, yawan littattafan da wannan dakin karatu ke da su ya riga ya kai miliyan 24 da dubu 110, wanda ya zo na biyar a tsakanin dakunan karatu a matsayin kasa a duk duniya, kuma adadin nan yana karuwa bisa dubu 600 zuwa dubu 700 a kowace shekara.

Jerin littattafai mafi tsufa da ake da su a cikin dakin karatu na kasar Sin su ne rubuce-rubucen da aka yi a kasusuwan dabbobi da kuma bayan kunkuru a shekaru fiye da 3000 da suka wuce. Bayan haka, dakin karatu na kasar Sin shi kuma dakin karatu ne da aka fi iya samun littattafan Sinanci a duk duniya da kuma dakin karatun da aka fi samun littattafan harsunan waje a nan kasar Sin. Ban da wannan, yana tattara wallafe-wallafen da kungiyoyin duniya da gwamnatoci dabna daban suka bayar, M.D.D. ya kuma danka masa nauyin ajiye takardunta.

Bisa sauye-sauyen hanyoyin watsa labarai da kuma cigaban hanyoyin sadarwa na zamani, ba ma kawai dakin karatu na kasar Sin ke da kananan abubuwan da ke dauke da bayanai da kayayyakin da ke dauke da bayanai na murya ko hoto, wato AV ba, yana kuma da sansanonin da ke dauke da bayanai, wato database na CD-ROM na gida da kuma waje kusan 100, ga shi kuma da wallafe-wallafe ta hanyar na'urorin zamani.

Dakin karatu na kasar Sin yana kuma da dakin karatu da ake amfani da na'urorin zamani, wato electronic reading library cikin Turanci,wanda ya fi girma a nan kasar Sin, wanda kuma ke da sansanonin da ke dauke da bayanai, wato database, da kuma wallafe-wallafe ta hanyar na'urorin zamani wadanda ke shafar ilmin zaman al'umma da kuma ilmin kimiyya.

Yayin da ake kara yin amfani da fasahohin na'urori masu kwakwalwa da kuma fasahohin internet, dakin karatu na kasar Sin ya kuma yi kokarin shigowa da fasahohin zamani a cikin ayyukansa daban daban, don neman gaggauta sauya kansa zuwa dakin karatu na zamani. Tun daga shekara ta 1995, dakin karatu na kasar Sin ya fara yin nazari a kan dakin karatu na zamani, wato digital library a bakin Turawa, kuma a shekara ta 2001, a hukunce ne majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta amince da aikin gina digital library na kasar Sin, gwamnatin kasar Sin ta kuma ware kudin da yawansa ya kai kudin Sin yuan biliyan 1 da miliyan 235 ga wannan aiki. (Lubabatu Lei)