Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-01-11 15:34:15    
Shugaban kwamitin wasannin Olympics na nakasassu na duniya ya sa ran alheri ga taron wasannin Olympics na nakasassu na Beijing

cri

Duk da kasancewar hasken taron wasannin Olympics, galibin mutane na kasa ganin fuskar taron wasannin Olympics na nakasassu. Amma darajar taron wasannin Olympics na nakasassu tana da muhimmancin gaske daidai kamar yadda taon wasannin Olympics yake. A wani fanni dai, mahalarta taron wasannin Olympics na nakasassu sun cancanci a fi girmama su. Idan dai ba a manta ba, an gudana da taron wasannin Olympics na nakasassu a karo na farko a shekarar 1960 a birnin Rome na kasar Italiya. Kuma tun daga shekarar 1988, an gudanar da taron wasannin Olympics da kuma taron wasannin Olympics na nakasassu a wuri daya. Ban da wannan kuma, yau da shekaru da dama da suka shige, kwamitin wasannin Olympics na kasa da kasa ya tsaida kudurin cewa, duk wani birnin da ya cimma nasarar samun damar gudanda da taron wasannin Olympics yana da alhakin gudanar da taron wasannin Olympics na nakasassu a lokaci daya.

Gwamnatin birnin Beijing wadda ta dauki nauyin gudanar da taron wasannin Olympics na yanayin zafi na karo na 20 da kuma taron wasannin Olympics na nakasassu na yanayin zafi na karo na 13 a shekarar 2008 ta fito da kirarin cewa " A gudanar da gagaruman tarurrukan taron wasannin Olympcs guda biyu masu ban sha'awa". Wannan dai ya kasance irin kyakkyawan fata ne da Malam Phillip Craven, dan asalin kasar Burtaniya kuma shugaban kwamitin wasannin Olympics na nakasassu na duniya ya nuna wa taron wasannin Olympics na nakasassu na Beijing.

An shiga mataki na biyu na sayar da tikitocin kallon wasannin Olympics na Beijing a wannan wata yayin da za a sayar da tikitocin kallon wasannin Olympics na nakasassu na Beijing. Kwanan baya dai, Mr. Craven ya kawo ziyara nan Beijing, inda ya yi kira ga jama'a masu tarin yawa na kasar Sin da su je filaye da dakunan gasanni don kallon wasannin nakasassu a shekara mai kamawa. Ya furta cewa:

" Lallai farashin tikitocin kallon wasanni ba shi da tsada, an kuma tsaida farashi irin na musamman domin 'yan makaranta yayin da ake la'akari da 'yan kallo masu shekaru daban-daban da haihuwa".