Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-01-10 22:05:06    
Samun jituwa a cikin unguwannin jama'a ta hanyar yin shawarwari

cri

An kafa unguwar Qinghe a shekaru 80 na karnin da ya gabata, inda ake iya samun mutane 6600, kuma fiye da kashi 90 cikin dari daga cikinsu ma'aikata ne. tsohuwar shugabar kwamitin kula da ayyukan unguwar Guo Zhaoxiong ta bayyana cewa, a shekaru 90 na karnin da ya gabata, dimbin mutane na unguwar sun rasa ayyukan yi, sabo da rashin gamsu da zamantakewar al'umma, su kan sha giya da kuma ta da tarzoma.

Domin warware rikici iri daban daban da ke cikin unguwar, a watan Yuni na shekara ta 2004, unguwar Qinghe ta fitar da tsarin warware matsaloli ta hanyar yin shawarwari, ta haka ta samu wata hanyar samun jituwa. Wang Aixia, shugabar kwamtin ta gaya mini cewa, an tsara wannan tsari ne domin tattara mazaunan unguwar da kuma tattaunawa kan harkokin unguwar, ta yadda za a iya warware wasu matsalolin da mazauna ke fuskanta. Ta aiwatar da tsarin, an warware matsaloli da rikicin mazauna a cikin unguwa, ta yadda za a iya samun kwanciyar hankali da kuma jituwa a unguwa.

Bayan da kafuwar tsarin shawarwari, mazaunan unguwar Qinghe suna ikon tattaunawa kan dukkan harkokin unguwar da na kansu, ta haka an kara kwarin gwiwar mazauna sosai wajen sa hannu a cikin ayyukan raya unguwa.

Kuma an labarta cewa. Tun bayan shekara ta 2004, kwamitin kula da harkokin unguwar Qinghe ya kira tarurukan tattaunawa fiye da 30 kan tsabta muhallin unguwar, da tabbatar da zaman lafiyar unguwar, da kuma ba da tabbaci ga zaman fararen hula mafi kankanta, da kuma sake samar da guraban aikin yi da dai sauransu, yawan mazaunan unguwar da suka halarci tarurukan ya kai 1200, wadanda suka gabatar da shawarwari fiye da 130. Kuma ana warware su sannu a hankali.