Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-01-10 17:53:32    
Sin za ta fi mai da hankalinta a kan jin dadin jama'a da kuma zaman daidaici a wajen gyaran tsarin kiwon lafiya

cri

A gun taron manema labarai da aka kira a yau 10 ga wata, kakakin ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Sin, Mr.Mao Qun'an ya bayyana cewa, gyara tsarin kiwon lafiya daga dukan fannoni wani muhimmin aiki ne a gaban sassan kiwon lafiya a shekarar da muke ciki, kuma a yayin da ake gyara tsarin kiwon lafiya, batun jin dadin jama'a da kuma zaman daidaici suna kan wani muhimmin matsayi.

Gyara tsarin kiwon lafiya matsala ce da ke gaban kasashen duniya baki daya. A watan Agusta na shekarar 2006, Sin ta kafa wata kungiyar aiki da ke kunshe da sassan gwamnati 16, don su hada kansu su yi bincike a kan batun gyaran tsarurruka, har ma su danka wa hukumomin musamman 7 na gida da na waje nauyin gudanar da bincike cikin gashin kansu, tare kuma da neman shawarwarin jama'a. A halin yanzu dai, an cimma ra'ayoyin jagoranci wajen gyaran tsarin kiwon lafiya, har ma za a zabi wasu wurare da su gudanar da gwaje-gwaje. Mr.Mao Qun'an, kakakin ma'aikatar kiwon lafiya ta Sin ya bayyana cewa, gyara tsarin kiwon lafiya daga dukan fannoni wani muhimmin aiki ne da ke gaban sassan kiwon lafiya a shekarar da muke ciki, ya ce,"ya kamata mu fahimci muhimmancin aikin gyaran tsarin kiwon lafiya da wuyarsa, sa'an nan, mu aiwatar da shirin da majalisar gudanarwa ta Sin za ta bayar nan gaba kadan dangane da zurfafa gyare-gyaren tsarin kiwon lafiya, da kuma gudanar da gwaje-gwajen gyaran yadda ya kamata."

A gun taron aikin kiwon lafiya na duk kasar Sin da aka rufe ba da jimawa ba, Mr.Chen Zhu, ministan kiwon lafiya na kasar Sin ya bayyana cewa, sassaucin tsarin kiwon lafiyar jama'a a fannin jin dadin jama'a ya riga ya zama wani babban batun da jama'a suka fi mayar da martani a kansa. A yayin da ake gudanar da gyare-gyaren tsarin kiwon lafiya, tilas ne a dora muhimmanci a kan jin dadin jama'a da kuma moriyar jama'a, ya ce,"harkar kiwon lafiya harka ce ta jin dadin al'umma da gwamnati take gudanarwa. Aikin kiwon lafiya shi ne kare lafiyar jikin jama'a da kuma sa kaimi ga bunksuwar jama'a daga dukan fannoni, a maimakon cin riba ta hanyar warkar da majiyyata."

Mr.Chen Zhu ya kuma yi nuni da cewa, tilas ne a mai da hankali a kan tsarin kiwon lafiyar jama'a da gwamnati ta shimfida a birane da garuruwa, a yayin da ake tabbatar da jin dadin al'umma a fannin kiwon lafiyar jama'a. A sa'i daya, ya kamata a aiwatar da manufar ba da taimako da gwamnati ta tsara, kazalika, ya kamata a kara zuba kudaden jari.

Zaman daidaici a fannin kiwon lafiya shi ma ya kasance wani abin da aka dora muhimmanci a kansa a wajen gyaran tsarin kiwon lafiya. A gun taron, kakakin ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Sin, Mr.Mao Qun'an ya bayyana cewa, a hakika, yanzu a kasar Sin, ya kasance da bambanci a tsakanin yankuna daban daban da kuma jama'a a fannin kiwon lafiya, wannan shi ma wata matsalar da ya kamata a daidaita a wajen gyaran tsarin kiwon lafiya. Ya ce,"zaman daidaici a fannin kiwon lafiya wani muhimmin fanni ne na zaman daidaici tsakanin al'umma. Muna gudanar da gyare-gyare, ta yadda a yayin da muke kafa tsarin jin dadin kowa da kowa a fannin kiwon lafiya, za mu mayar da samun kiwon lafiya cikin daidaici a matsayin wani muhimmin burin da za a cimmawa."(Lubabatu)