Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-01-09 15:28:24    
Kasar Sin tana kokarin kare kayayyakin tarihi na duniya

cri

A gun taro na karo na 28 da hukumar kula da kayayyakin tarihi ta duniya ta shirya, an mayar da garin sarkin Gaojuli da gine-ginensa na kasar Sin don ya zama daya daga cikin kayayyakin tarihi na duniya, ta haka yawan kayayyakin tarihin duniya ya karu zuwa 30 a kasar Sin. An sha yin tambaya cewa, yaya za a kare wadannan kayayyakin tarihi masu daraja na dan adam da kuma kula da su?

A shekarar 1972, Kungiyar UNESCO ta Majalisar Dinkin Duniya ta zartas da "yarjejeniyar kare kayayyakin tarihi na duniya". Kasar Sin ta sa hannu a kan wannan yarjejeniya ne a shekarar 1985. Ban da kasar Sin tana da wadannan kayayyakin tarihi na duniya da yawansu ya kai 30 kamar Kogon Dutse mai suna Dunhuang da Dutsen Huangshan da Dutsen Taishan da sauransu, yanzu kuma ta shirya misalin kayayyakin tarihi 100 don su zama na duniya, saboda haka kasar Sin ta zama daya daga cikin kasashe da suke neman mayar da kayayyakin tarihinsu masu yawa don su zama irin na duniya.

Madam Fan Jinshi, shugabar cibiyar binciken Kogon Dutse na Dunhuang wadda ke kula da harkokin kare wannan wurin tarihi na duniya ta bayyana cewa, " yawan masu yawon shakatawa da ke ziyartar wadannan wuraren al'adu na tarihi ya yi yawan gaske, mai yiwuwa ne wannan zai kawo lahani ga wadannan wurare. "

Wannan al'mari ya riga ya jawo hankalin hukumomi da abin ya shafa na kasar Sin. Malam Guo Zhan, shugaban sashen kula da kayayyakin tarihi na duniya na hukumar kula da harkokin kayayyakin tarihi ta kasar Sin ya bayyana cewa, " kasar Sin makekiyar kasa ce, matsayin ci gaba da aka samu a fannin tattalin arziki da na al'adu ya sha bamban a wurare daban daban na kasar. Ko da yake mun yi kokari sosai wajen kare kayayyakin tarhi na kasarmu, amma duk da haka mun gamu da wasu matsaloli wajen kare su."

Yanzu ana nan ana neman daidaita wadannan matsaloli. Hukumar kare kayayyakin tarihi ta kasar da ma'aikatar gine-gine ta kasar da kuma sauran hukumomi da abin ya shafa sun sha shirya tarurruka don yin nazari a kan shirin da za a tsara don kare kayayyakin tarihi na duniya bisa halin da ake ciki a kasar Sin. Haka nan kuma tun daga gwamnatin kasar Sin har zuwa kananan hukumomi na wurare suna kara kashe kudade wajen yin kwaskwarima a kan kayayyakin tarihi na duniya. Malam Mei Ninghua, shugaban hukumar kare kayayyakin tarihi ta birnin Beijing ya bayyana cewa, "a shekarar bara, an bayar da shirin birnin Beijing a fili dangane da yin kwaskwarima a kan wuraren tarihin duniya guda 6 da kuma kare su. Yanzu kuma an riga an fara yin kwaskwarima a kan Babbar Ganuwa da Fadar Bazara da Dakin Addu'ar Neman Girbi Mai Armashi na Lambun Shan Iska da ake kira "The Temple Of Heaven" cikin Ingilishi da kuma sauran wuraren tarihi da ke nan birnin Beijing. Yawan kudi da aka kashe wajen yi wa wadannan wuraren tarihi na duniya kwaskwarima ya yi yawa har ba a taba ganin irinsa ba a da."

Daidai kamar yadda aka yi a nan birnin Beijing, a sauran wurare na kasar kuma ana kara yin kokari wajen kare kayayyakin tarihi na duniya. Musamman ma a cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, an yi ayyuka masu yawa wajen karantar da jama'a yadda ake kare kayayyakin tarihi na duniya da kuma muhimmancinsu, ta haka ne jama'a suke kara mai da hankulansu ga kare kayayyakin tarihi.

Yanzu, bangarorin kare kayayyakin tarihi na kasar Sin suna kara samun ra'ayi daya a kan karuwar yawan kayayyakin tarihin duniya a kasar. Ra'ayin nan shi ne nasarar da aka samu wajen amincewa da kayayyakin tarihin duniya masu yawa a kasar Sin, ta sa kaimi ga kare duk kayayyakin tarihi da ni'imatattun wuraren al'adu da kuma sauran shahararrun wuraren yawon shakatawa a kasar. Ya kamata, mu kare wadannan wurare da kayu wadanda na duk 'yan adam ne kuma ba a iya sake kago su ba.

Malam Guo Zhan, shugaban sashen kayayyakin tarihin duniya na hukumar kula da harkokin kayayyakin tarihi ta kasar Sin ya bayyana cewa, shigar da kayayyakin tarihi da shahararrun wuraren yawon shakatawa na kasar Sin cikin sunayen kayayyakin tarihin duniya abin alfahari ne gare mu, amma babbar manufar da muke bi ita ce don kare wadannan kayayyakin tarihi da shahararrun wurare na kasar Sin da kyau.