Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-01-09 14:45:10    
Kasashen Afirka na dukufa wajen warware batun Darfur cikin ruwan sanyi

cri
A shekarar bara, saboda ayyukan shiga tsakani da bangarori suka yi, kasashen duniya sun fito da hanyar warware batun Darfur na kasar Sudan sannu a hankali. A wani bangare, Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar tarayyar Afirka wato AU sun kaddamar da aikin kiyaye zaman lafiya cikin hadin gwiwa a yankin Darfur. A wani daban kuma, gwamnatin kasar Sudan da rukunonin Darfur da ba sa ga maciji da gwamnatin sun maido da shawarwarin zaman lafiya a birnin Surt da ke bakin teku a kasar Libya a ran 27 ga watan Oktoba na shekarar bara. In an kwatanta da kasashen duniya da ke kokarin warware wannan batu cikin lumana, kasashen Afirka sun fi taka muhimmiyar rawa.

A shekarar bara, an mai da hankakli kan ja-in-ja a tsakanin bangarorin da abin ya shafa a kan batun kiyaye zaman lafiyar Darfur. Bisa yarjejeniyar tsagaita bude wuta da gwamnatin Sudan da dakarun Darfur da ke adawa da gwamnatin suka daddale a birnin Ndjamena, hedkwatar kasar Chadi a watan Afrilu na shekarar 2004, kungiyar AU ta tura sojoji dubu 7 domin kiyaye zaman lafiya a Darfur. Wannan shi ne karon da kungiyar AU ta fi tura dimbin sojoji domin wanzar da zaman lafiya bayan kafuwarta.

Bayan da sojojin kiyaye zaman lafiya na kungiyar AU suka shiga yankin Darfur, sun taka rawa wajen sa aya ga rikici da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, amma cikin gajeren lokaci sun nuna abubuwan kasawa da aka samu a sakamakon yin karancin kudi da injunan soja. Ban da wannan kuma, kungiyar AU ta nemi kasashen duniya da su ba da taimako da goyon baya, amma kasashen duniyar yamma da suka hada da kasar Amurka sun yi amfani da wannan zarafi, sun nemi rundunar kiyaye zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya da ta maye gurbin takwararta na kungiyar AU.

A karshe dai, bisa tushen shiri na matakai 3 da Kofi Annan, tsohon babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya gabatar, bangarorin da abin ya shafa sun cimma daidaito kan kiyaye zaman lafiya a Darfur cikin hadin gwiwar Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar AU. A watan Yuli na shekarar bara, kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya zartas da kuduri mai lamba 1769, inda ya tsai da kudurin jibge sojoji dubu 26 domin wanzar da zaman lafiya cikin hadin gwiwa a Darfur.

Gwamnatin Sudan da kungiyar AU suna tsayawa tsayin daka kan cewa, kasashen Afirka sun sami rinjaye a cikin wannan hadaddiyar rundunar kiyaye zaman lafiya. Shugaba Omer Hassan Ahmed Elbashir na Sudan ya nuna cewa, bisa yarjejeniyar da bangarorin da abin ya shafa suka daddale, ban da wasu kasashen duniya da suka hada da Sin da Bangladesh sun aika da sojojinsu na ba da tabbacin guzuri, yawancin mambobin rundunar sun zo daga kasashen Afirka.

Kasashen Afirka sun taka muhimmiyar rawa wajen wanzar da zaman lafiya a Darfur. Shugaban kungiyar AU da manzon musamman na kungiyar AU mai kula da batun Darfur malam Salim Ahmed Salim sun sha shiga tsakani, suna bayar da kokari domin daidaita batun Darfur cikin lumana. Kasashen Libya da Masar da Chadi da Eritrea da sauran kasashen Afirka sun shirya tattaunawa a tsakanin kungiyoyin Darfur da ke adawa da gwamnatin sau da yawa, sun nemi daidaita matsayinsu domin samar da sharadi wajen yin shawarwarin zaman lafiya. Sa'an nan kuma, kasashen Afirka da suke makwabtaka da Darfur sun karbi dimbin 'yan gudun hijira, sun ba da babbar gudummowa wajen sassauta rikicin akidar jin kai.

Abin da ya kamata a lura da shi shi ne saboda batutuwan da take fuskanta a gida da kuma a waje, Sudan tana fuskantar sarkakkiyar batun Darfur, ba ta iya warware shi ba cikin sauri.

Bisa kyawawan fasahohi da aka samu a da, tsarin yin shawarwari a tsakanin Sudan da kungiyar AU da Majalisar Dinkin Duniya zai ci gaba da taka rawa mai yakini wajen daidaita batun Darfur, a ciki kuma kada a nuna rashin kulawa kan rawar kungiyar AU. Da farko, batun Darfur ya shafi moriyar Sudan da sauran kasashen Afirka. Kabilu da yawa na wurin suna da nasaba da sauran kasashen Afirka. Kazalika kuma, wasu kasashen Afirka sun sha wahalar rikicin Darfur. Shi ya sa ba za a iya warware batun Darfur ba, in kasashen Afirka ba su shiga ayyukan daidaita wannan batu ba.(Tasallah)