Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-01-09 14:20:34    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki(03/01-09/01)

cri
A gun taron shugabannin hukumomin wasannin motsa jiki na kasar Sin na shekarar 2008 da aka bude a ran 7 ga wata, Liu Peng, shugaban hukumar wasannin motsa jiki ta kasar Sin ya sake jaddada cewa, 'yan wasan Sin suna fuskantar hali mai tsanani wajen share faren gasar wasannin Olympic ta Beijing ta shekarar 2008.

Wannan jami'in Sin ya kara da cewa, bisa ci gaba da sauye-sauyen da aka samu a shekarun baya, 'yan wasa na kasashe da yankuna daban daban na duniya sun inganta karfinsu wajen share fagen gasar wasannin Olympic sannu a hankali, sun kara kyautata makinsu a kwana a tashi. Ba za su nuna dukkan ainihin karfinsu ba sai sun shiga mataki na karshe. Bisa halin da kasar Sin ke ciki a harkokin wasanni, ko da yake ta sami ci gaba a wasu shirye-shirye, ta kuma kyautata karfinsu kadan, amma tana fuskantar matsaloli, a wasu shirye-shirye kuma tana gamuwa da manyan matsaloli.

Malam Liu ya sake nanata cewa, dole ne 'yan wasan Sin su kasance cikin natsuwa, su gano hali mai tsanani wajen shiga gasar wasannin Olympic ta Beijing da babban nauyinsu da kuma takara mai tsanani da za su fuskanta.

Kazalika kuma, malam Liu ya fayyace cewa, a shekarar bara, kasar Sin ta sami kyakkyawar nasara wajen yaki da amfani da magani mai sa kuzari. An yi bincike kan 'yan wasan Sin dubu 10 da 238 a fannin yin amfani da magani mai sa kuzari a duk shekarar bara, irin wannan adadi ya karya matsayin bajimta a tarihin kasar Sin. A ciki kuma, an gano 'yan wasan Sin 15 da suka yi amfani da magani mai sa kuzuri, yawan masu amfani da magani mai sa kuzari bai kai kashi 0.2 cikin kashi dari ba bisa jimlar 'yan wasan da aka yi musu bincike. Kasar Sin tana cikin matakin da yawan masu amfani da magani mai sa kuzari ya fi yin kasa a tarihinta.

Bayan da ta sake yin ziyarar aiki a kasar Sin a watan Satumba a shekarar bara, tawagar hukumar yaki da magani mai sa kuzari ta kasa da kasa wato WADA ta nuna babban yabo kan nasarorin da kasar Sin ta samu wajen yaki da magani mai sa kuzari.

Ran 5 ga wata, aka rufe gasar wasan gudun Marathon ta kasa da kasa a shekarar 2008 a birnin Xiamen na kasar Sin. 'Yar wasa Zhang Yingying ta kasar Sin ta zama zakara a cikin rukuni na mata. Sauran 'yan wasa 2 na kasar Sin sun zama na biyu da na uku a tsakanin mata.

A cikin rukuni na maza kuwa, dan wasa Deng Haiyang na kasar Sin ya zama na uku bisa maki mafi kyau da ya samu. 'Yan wasan kasar Kenya 2 sun zama na farko da na biyu.

Ran 4 ga wata, hadaddiyar kungiyar wasan kwallon tebur ta kasa da kasa ta kaddamar da jerin sunayen 'yan wasa na kasa da kasa a karo na farko a shekarar da muke ciki, wannan ya nuna cewa, an fito da jerin sunayen 'yan wasan da za su shiga gasar wasannin Olympic ta Beijing kai tsaye a rukuni na farko. Bisa wannan jerin sunaye, 'yan wasa Wang Hao da Ma Lin da Guo Yue da kuma Zhang Yining na kasar Sin da suka zama na farko da na biyu a tsakanin maza da kuma a tsakanin mata a duniya za su shiga gasar wasannin Olympic ta Beijing kai tsaye.(Tasallah)