
Game da batun samar da abinci a wasan Olympic na Beijing na shekarar 2008, mataimakin ministan noma na kasar Sin Gao Hongbin ya furta a ran 8 ga wata a nan birnin Beijing cewa, kasar Sin za ta samar da galibin abincin wasan Olympic, sabo da haka ma'aikatar noma ta kasar za ta dauki matakai don ba da tabbaci ga samar da ingantaccen abinci ga wasan Olympic.
A ran nan, a gun taron manema labaru da ofishin yada labaru na majalisar gudanarwa ya yi, Gao Hongbin ya ce, ma'aikatar noma da kananan gwamnatocin jihohi 13 ciki har da gwamnatin Beijing za su hada kansu sun aiwatar da ayyuka don tabbatar da samar da ingantaccen amfanin gona ga wasan Olympic.(Lami)
|