Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-01-08 15:28:34    
wasu yaran da ke yankunan dutse, wadanda suka fito daga manyan duwatsu zuwa birane don samun ilmi a sakandare

cri

Fu Qin da ke da shekaru 14 na haihuwa tana zama tare da iyalinta a dutsen Longquan na yankin Long Quan Yi Qu na birnin Chengdu da ke kudu maso yammacin kasar Sin. A lokacin da take karatu a firamare, iyayenta sun soma aiki a waje, saboda haka, Fu Qin da kanwarta suna zama tare da kakanninsu. Fu Qin ta yi karatu a wani firamaren da ke yankin dutse har shekaru 6. Ta gaya mana cewa,

"Makarantarmu tana wurin da ke da wuyar zuwa, akwai dalibai sama da 100 kawai a ciki, yawan malamai ya kai kusan goma. Kullum dakunan aji suna yoyo a yanayin ruwa."

Ko da ya ke Fu Qin ta sha wahala sosai, amma ta yi kokari kan karatunta, har ma ta gama karatunta a firamare kamar yadda ya kamata. Amma, iyalinta ya gamu da matsala, wato babu makarantun sakandare a shiyyoyin da ke kusa da gidansu, kuma iyalin nan ba ya da isasshen kudi, don biyan kudin dakin kwana. A lokacin da Fu Qin ke nuna damuwa kan wannan, wani malaminta ya gaya mata wani labari mai kyau.

"Ya gaya mana cewa, yanzu gwamnatinmu ta fito da wasu manufofin gatanci. Aiwatar da aikin "zinarin Phoenix", wannan ne manufa daya daga cikinsu, wato idan mu samu sakamako mai kyau wajen karatu, to, za mu samu damar yin karatu a birane."

Bisa tatsuniyar da aka bayar a kasar Sin an ce, Phoenix, wane irin tsuntsun da ke nuna alheri, Sinawa su kan kwatanta "Zinarin Phoenix" tamkar kwararrun da suka samu nasara daga muhalli mai wuya. Aikin "Zinarin Phoenix" da Fu Qin ta ambata, shi ne wani matakin da aka dauka, domin shigar da daliban da ke yankunan manyan duwatsu cikin birane, don samun ilmi.

Yanzu, an riga an soke dukkan makarantun sakandare da ke yankin Long Quan Yi Qu, daliban da ke yankin sama da 3100, ciki har da Fu Qin, dukkansu sun shiga makarantun sakandare na birane. Ba kawai za su samu gatanci wajen samun ilmi mai nagarta ba, har ma za su samun kudin tallafi na abinci RMB 100, da na sufuri RMB 20, da kuma ruwan sha RMB 10 a ko wane wata.

Makarantar sakandare da Fu Qin ke karatu a yanzu, ita ce wata makarantar da ke da dakunan kwana. An soma kafa makarantar tun daga watan Janairu na shekarar 2007, kuma ta soma aiki a watan Satumba na shekarar. Azuzuwa, da ginin kwana, da filin motsa jiki, da kuma ofisoshin gwaji da na kamputa, da dai sauransu, dukkansu sun jawo hankulan mutane sosai.

Ban da wannan kuma, makarantar ta zabi malamai masu inganci. Shugaban makarantar Mr. Zhang Yulin ya gabatar da cewa,

"Yawancin malaman makarantarmu sun fito ne daga kwararrun da aka zaba a dukkan yankin Long Qun Yi Qu, wasu kuma su ne malamai masu kyau na sauran wurarre, kar ma mun zabi daliban da suka gama karatu daga jami'o'i."

Malaman makarantar sun gaya wa wakilinmu cewa, ta hanyar aiwatar da aikin "Zinarin Phoenix", daliban yankunan duwatsu sun samu ci gaba a dukkan fannoni. Yanzu, sun riga sun dace da ka'idojin aikace-aikace na zaman rayuwar jama'ar birane.

Nan gaba kuma, yankin Long Quan Yi Qu zai shigar da wasu daliban firamare zuwa birane, a lokacin, yaran yankunan duwatsu da yawa za su iya samun ilmi kamar iri na yaran da ke birane.(Kande Gao)