Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-01-08 15:26:15    
Wasu labaru game da kabilun kasar Sin

cri
---- Mun sami labari daga gwamnatin jihar Mongoliya ta gida mai ikon tafiyar da harkokin kanta ta kasar Sin cewa, a wannan shekarar da muke ciki, jihar Mongoliya ta gida ta daidaita matsalar karancin ruwan sha mai inganci ga manoma da makiyaya wadanda yawansu ya kai dubu 760. wato ta cika alkawarin da ta dauka wajen magance matsalar karancin ruwan sha ga mutane dubu 600 a duk shekara.

Bisa matsayinta na jihar da ke fama da fari, ko kuma jihar da ba a samu ruwan sama sosai ba, jihar Mongoliya ta gida ta kasar Sin tana fama da karancin ruwa sosai, wannan ya jawo mummunar illa ga aikin kawo albarka da zaman rayuwa na manoma da makiyaya. Bisa shirin da aka tanada an ce, daga shekarar 2006 zuwa ta 2010, za a daidaita matsalar karancin ruwan sha mai inganci ga mutane fiye da miliyan 4.2 na jihar, kuma za a shafe shekaru kusan 10 don daidaita matsalar karancin ruwan sha mai inganci a shiyyoyin noma da kiwon dabbobi ta hanyar jawo ruwa da nisa da diban ruwa daga karkashin kasa.

---- Kwanan baya yayin da Mr. Li Xuansheng, sakataren kwamitin yankin Huangnan na kabilar Tibet mai ikon tafiya da harkokin kansa da ke lardin Qinghai na kasar Sin yake amsa tambayoyin da manema labaru ya bayyana cewa, gundumarsa tana kokarin kaddamar da tambarin "al'adun Regong" ta hanyar dogara bisa sigar musamman ta al'adun kabilun dake wannan wuri.

"Al'adun Regong" wani muhimmin kashi ne daga cikin al'adun addinin Buddha na Tibet, wanda ya samo asali tun a karni na 13 daga gundumar Tongren ta yankin Huangnan na kabilar Tibet mai ikon tafiya da harkokin kansa da ke lardin Qinghai, cikin daruruwan shekaru da suka gabata, yawancin maza na wannan wuri suna gadon fasahar zane-zanen addinin Buddha wadda ta samu yaduwa daga wuraren addinin Buddha zuwa zaman al'umma, sabo da haka ana darajanta gundumar da sunan "garin zane-zanen Tibet". Yan zuwa yanzu, yawan sassan al'adun Regong da ake da su a gundumar Tongren ya kai kusan 100, wadanda suke da ma'aikata fiye da 2,000, matsakaicin yawan masu yawon shakatawa da suka kai ziyara ya wuce dubu 190 a kowace shekara.

---- Yanzu kayayyakin musamman na jihar Tibet suna ta kara ba da babban taimako ga jihar wajen gaggauta ci gaban tattalin arzikin jihar, kuma sun riga sun zama muhimmiyar hanya ga manoma da makiyayan jihar Tibet domin kara samun kudin shiga da yawa.

Wakilinmu ya sami labari daga wajen taron manema labaru da gwamnatin jihar Tibet mai ikon tafiya da harkokin kanta ta yi a ran 12 ga wata an ce, kayayyakin musamman da aka fitar daga jihar Tibet da wadanda aka sayar da su suna da yawan gaske. Yawan irin maganin da ake kira "Dongchongxiacao" kawai da aka diba a wannan shekara a duk jihar ma ya wuce Ton 50, yawan karin kudin shiga da manoama da makiyaya suka samu kai tsaye ya kai fiye da kudin Sin wato Yuan biliyan 4.