Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-01-07 21:09:58    
Aikin shirya kyakkyawar gasar wasannin Olympics ya fi kome muhimmanci da birnin Beijing zai yi a bana

cri
Yayin da shugaban majalisar bada shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin Jia Qinglin ke gudanar da aikin bincike a nan birnin Beijing, ya jaddada cewar, kamata ya yi a sanya aikin shirya gasar wasannin Olympics da kyau, a matsayin wani abin da ya fi kome muhimmanci, yayin da birnin Beijing ke tafiyar da harkokinsa a shekarar da muke ciki. Haka kuma, ya kamata a sanya iyakacin kokari wajen aiki bisa madaukakin ma'auni, domin tabbatar da cimma nasarar shirya gasar wasannin Olympics.

Bugu da kari kuma, Mr. Jia ya jaddada cewar, gwamantin tsakiya ta kasar Sin ta dade tana maida hankalinta sosai kan ayyukan share-fagen gasar wasannin Olympics ta Beijing. Kamata ya yi birnin Beijing ya kara kyautata tsarin sana'o'insa, da yin namijin kokari domin raya sana'ar bada hidima ta zamani, da maida hankali sosai dangane da ayyukan yin tsimin makamashi da rage gurbataccen hayaki da ake fitarwa, da daga matsayin aikin raya birni da aikin bada hidima, ta yadda za a tabbatar da akidar gasar wasannin Olympics, wato "gasar wasannin Olympics dake da muhalli mai kyau, da gasar wasannin Olympics dake da kimiyya da fasaha, da gasar wasannin Olympics dake da nagartattun al'adu".(Murtala)