Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-01-07 20:04:23    
Kasar Sin za ta ba da tabbaci kan kiwon lafiyar jama'a a lokacin wasannin Olympic na Beijing

cri
Yau 7 ga wata, ministan kiwon lafiya na kasar Sin Mr. Tian Zhu ya bayyana a nan birnin Beijing cewa, a shekarar 2008, kasar Sin za ta kara daukar matakan ba da tabbaci kan kiwon lafiya, ciki har da duduba cututtuka, da sa ido kan kiwon lafiya, da magance kiwon lafiya cikin gaggawa, da kuma yin jiyya, da dai sauransu, domin ba da tabbaci ga yanayin kiwon lafiya a lokacin wasannin Olympic da na nakasassu.

Mr. Chen ya ce, za a shirya wasannin Olympic da na nakasassu a nan birnin Beijing, wannan ne wata babbar dama mai kyau ga bunkasuwar kiwon lafiyar jama'a ta kasar Sin. Kasar Sin za ta karfafa hadin gwiwa a tsakanin biranen da za su shirya wasannin Olympic, ciki har da birnin Beijing, da kuma jihohin da ke makwabtaka da su, don yin rigakafi da shawo kai, da kuma duduba bayanai kan cututtuka daga kasashen waje, bugu da kari kuma, kasar Sin za ta yi gwaji da kuma kyautata shirin kuduri, domin yin rigakafi, da rage, da kuma kawar da hadarin kiwon lafiyar jama'a. (Bilkisu)