Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-01-07 09:43:39    
Birnin Olympia na kasar Greece yana kokarin tabbatar da ganin birnin Beijing ya dauki wuta mai tsabta

cri

A ran 6 ga wata, magajin birnin Olympia na kasar Greece Giorgos Aidonis ya gaya wa Luo Linquan, jakadan kasar Sin da ke kasar Greece wanda ya kai ziyara ga birnin Olympia, cewar birnin Olympia zai gama aikin dasa itatuwa cikin lokaci, kuma zai yi namijin kokarinsa wajen farfado da tsire-tsiren da ke kewayen kangon Olympia da aka kona shi a kwanan baya domin tabbatar da ganin birnin Beijing na kasar Sin ya dauki wuta mai tsabta domin gasar wasannin motsa jiki ta Olympics ta shekarar 2008.

Tun daga ran 5 zuwa ran 6 ga wata, jakada Luo Linquan ya yi rangadin aiki a birnin Olympia domin share fagen aikin daukar wuta mai tsabta domin gasar wasannin motsa jiki ta Olympics ta Beijing. A rakiyar magaji Aidonis, ya kai ziyara ga wurin da za a dauki wuta mai tsabta da hanyar gudu da yola, da dakin ajiye kayayyakin tarihi na tsohon gasannin Olympics da dakin ajiye kayayyakin tarihi na gasannin Olympics na yanzu da otel-otel da ayyukan yawon shakatawa da dai sauransu.

A watan Agusta na shekarar da ta gabata, an samu wata babbar gobara a gandun daji na kasar Greece. Wannan gobara ta kona wasu tsire-tsire na kangon Olympia. Bisa al'adar da aka saba yi, za a dauki wuta mai tsabta a kangon Olympia a ran 24 ga watan Maris domin gasar wasannin motsa jiki ta Olympics ta Beijing. (Sanusi Chen)