Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-01-07 17:18:21    
Kafofin watsa labaru za su kara sanya ido a kan yadda ake kiyaye muhalli da albarkatun kasa a Sin

cri

A kwanan baya, a birnin Haikou na lardin Hainan da ke a kudacin kasar Sin, an shirya taron tattaunawa a kan zagayowar ranar cika shekaru 15 da aka da fara yin harkokin kiyaye muhalli na karni a kasar Sin. A gun taron, Malam Redi, mataimakin shugaban zaunannen kwamiti na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ya bayyana cewa, aikin kiyaye muhalli da albarkatun kasa wani aikin gaggawa ne ake yi cikin dogon lokaci, kafofin watsa labaru za su kara sanya ido a kan yadda ake kiyaye muhalli da albarkatun kasa a wurare daban daban na kasar Sin, don sa kaimi ga samun ci gaba mai dorewa wajen bunkasa harkokin tattalin arziki da zamantakewar al'umma.

Harkokin kiyaye muhalli na karni a kasar Sin manyan harkokin farfaganda ne a kan kiyaye muhalli da kwamitin kiyaye muhalli da albarkatun kasa na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da babbar hukumar kiyaye muhalli ta kasar da hukumar kula da gandun daji ta kasar da kuma sauran hukumomi sama da 10 suka fara shiryawa cikin hadin gwiwarsu a shekarar 1993, kuma manyan kofofin watsa labaru na kasar sama da 10 sun halarta. Bisa kidayar da aka yi, an ce, manema labaru wadanda suka halarci wadannan harkoki ya wuce dubu 30 a jihohi daban daban na kasar Sin, yawan bayanoni da na labaru da suka bayar ya zarce dubu 100.

Malam Redi, mataimakin shugaban zaunannen kwamiti na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ya kara da cewa, yayin da ake bunkasa harkokin tattalin arziki da zamantakewar al'umma cikin sauri a kasar Sin, yana kasancewa da wasu abubuwa marasa kyau kamar ra'ayin bunkasuwa da hanyoyin bunkasawa sun yi baya-baya, da tsarin masana'antu ba shi da kyau da sauransu. Sabo da haka, yayin da ake ci gaba da yin harkokin kiyaye muhalli na karni a kasar Sin, kamata ya yi, kafofin watsa labaru su kara sanya ido a kan yadda ake kiyaye muhalli da albarkatun kasa. Ya ce, "wajibi ne, a ci gaba da zurfafa harkokin kiyaye muhalli na karni a kasar Sin bisa sabon halin da ke ciki. Aikin kiyaye muhalli da albarkatun kasa wani aikin gaggawa ne da ake yi cikin dogon lokaci. Sabo da haka an bukaci hukumomin shari'a da kafofin watsa labaru da jama'a da su hada kansu su taka muhimmiyar rawa wajen sanya ido a kan yadda ake kiyaye muhalli da albarkatun kasa, sa'an nan kuma su yi kokarin zaman kyawawan masu yin farfaganda da masu aikatawa a fannin kiyaye yanayin kasa."

Bayan haka Malam Redi ya ci gaba da cewa, a cikin shekarun nan biyar da suka wuce, an sami kyakkyawan sakamako wajen gudanar da harkokin kiyaye muhalli na karni don sa kaimi ga raya zamantakewar al'umma mai tsimin makamani da kiyaye muhalli.

Malam Ye Rutang, mtaimakin shugaban hukumar kiyaye muhalli da albarkatun kasa ta majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ya bayyana cewa, don aiwatar da manufar raya kasa ta hanyar kimiyya da gwamnatin kasar Sin ta gabatar, ya kamata, a dora muhimmanci ga bayar da labaru a kan wannan manufar, yayin da ake gudanar da harkokin kiyaye muhalli na karni a kasar Sin a shekarar nan. Ya kara da cewa, "na daya, wajibi ne, a bayar da labaru musamman kan yadda ake kiyaye filaye da ruwa da ma'adinai da daji da teku da sauran albarkatu da kuma yin amfani da su kamar yadda ya kamata, a sa kaimi ga wurare daban daban da muhimman masana'antu da su aiwatar da aikin tsimin makamashi da rage fitar da abubuwa masu gurbata muhalli, don cim ma manufar tsimin makamashi. Na biyu, a bayar da labaru musamman a kan yadda ake hana gurbata ruwa da sararin sama da kasa, a sa kaimi ga wurare daban daban da muhimman masana'antu da su aiwatar da nauyin da ke bisa wuyansu na rage fitar da abubuwa masu gurbata muhalli, ta yadda za a sami kyakkyawan sakamako wajen kiyaye muhalli a bayyane." (Halilu)