Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-01-03 16:35:48    
Labaru masu ban sha'awa na kasar Sin(13)

cri
Masu kishin zaman lafiya na Japan sun kai ziyara a kasar Sin. A ranar talata da ta shige,tsofaffi goma sha daya na Japan sun kai ziyara a birnin Qingdao na lardin Shandong na kasar Sin sun yi wannan ziyara ne duk domin samun shaidun laifuffuka da sojoji mahara na Japan suka aikata a shekarun 1930. yawan shekarunsu na tsakanin 64 da 81 da haihuwa,dukkansu 'yan kungiyar masu kishin zaman lafiya a Japan. Sun gana da Mr Zhang Shufeng,wani manazarin ilimin tarihi kan harin da Japan ta kai wa kasar Sin na cibiyar nazarin ilimin zamantakewa ta birnin Qingdao. Mr Zhang ya yi musu bayani na tsawon sa'o'I uku da nuna musu hotunan da aka dauka kan mugunta da sojoji mahara na Japan suka aikata. Masu kishin zaman lafiya sun ce ba daidai ba ne mutanen Japan suka yi watsi da laifuffukan da sojojinsu suka aikata a tarihi.

Wata mace ta sami aure sabo da makullita ya bace. An sami wata mace a birnin Qingdao na lardin Shandong dake gabashin kasar Sin wadda makullita ya bace ba ta iya shiga gidanta ba,sai ta buga waya zuwa ga wani kamfanin kula da harkokin makulli.Kamfanin ya tura wani saurayi mai hikima. Da ya zo ya nuna iyawarsa ya bude kofar wannan mace cikin lokaci,hankalin macen ma ta kwanta. Da ta ga kwarewarsa a fannin makulli da kuma hikimarsa da hakurin da ya ke da shi, hankalinta ya juya zuwa saurayi. Daga baya suka shiga soyayya, a makon da ya shige sun yi aure,mutanen gari na farin ciki da cewa "bacewar makulli ta kawo mata miji. "

An kashe wani kare sabo da ya hadiye kudi.An sami wani tsohon manomi mai suna Yin a gundumar Wuyang ta lardin Anhui na kasar Sin.Bayan da ya sayar da amfanin noma ya samu kudin Sin RMB Yuan dubu da dari.Bai ajiye kudinsa a cikin banki ba sai ya sa kudin a cikin wata jakar roba tare da sauran takardu masu muhimmanci, ya boye shi a wani wurin da ya san shi kawai. A makon da ya shige ya je wurin da ya boye jakar kudi bai ga jakar ba,ya kasa hakuri ya nemi jakar a ruwa a jallo duk da haka bai gan jakar ba.A wannan lokaci ya ga karensa yana yayyaga takardu masu muhimmanci da ya cusa a cikin jakar. Yana tsammanin karen ya hadiye kudinsa sai ya kashe karen a cikinsa ya samo kudinsa.

Wani malami mai suna Gao Yafei wanda ya ke da digirin MBA ya kafa gandun kiwo dabbobi. Wani malamin koyarwa a jami'a da ya kammala karatunsa a jami'a ya sami digirin MBA. Duk da haka bai gamsu da aikinsa ba yana so ya kafa wani gandun kiwo dabbobi. A shekarar bara ya yi murabus daga aikinsa ya koma wurin da aka haife shi a lardin Anhui,Ya yi amfani da kudin Sin RMB Yuan kimanin miliyan biyu, daga cikinsa Yuan dubu dari tara ya yi aro ne daga banki. Ta haka ya kafa wani gandun kiwo dabbobi. Malamin nan ya yi karatun ilimi na na'ura mai kwakwalwa a jami'a ya kware a fannin,sai ya yi amfani da ilimin da ya samu,ya yi amfani da na'urori masu kwakwalwa wajen kiwo dabbobi ya kan bincike abincin dabbobi da kuma lafiyarsu ya kan rubuta bayanai a cikin na'urori ya kwatanta su. Bayan shekara guda fadin gandunsa ya kai muraba'in mita dubu sha biyu,yanzu yana nan yana kokarin mayar da gandunsa a matsayin koli na kasa baki daya.

Wani namiji ya biya kudin Sin Yuan dubu dari sabo da alkawarin da ya dauka. An sami wani mutum mai suna Li a birnin Zhengzhou na lardin Henan da ke tsakiyar kasar Sin. Mutumin nan ya yi da-na-sani domin alkawarin da ya dauka na biya kudin diyya kudin Sin Yuan dubu dari ga masoyiyyarsa idan ya rabu da ita. A ranar talata da ta shige, kotun jama'a ta tsakiya ta birnin Zhengzhou ta yanke hukuncin biya kudin Yuan dubu dari sabo da alkawarin da ya dauka ha yanzu yana da amfani.Wannan namiji yana da shekaru 31 da haihuwa ya shiga soyayya da budurwa mai suna Xu a shekara ta 2001,a shekara ta 2002 su yi zaman tare. A shekara ta 2003 sun rabu da juna,a wannan lokaci aka bukace shi da ya rubuta alkawarin biya kudin diyya ga budurwa. A shekara ta 2006,budurwa ta kai kara ga kotun kan alkawarin da wannan namijin ya rubuta mata. Daga bisani kotun ta yanke hukuncin biya kudin diyya kudin Sin Yuan dubu dari ga budurwa.

Wani karamin yaro yana so ya zama dan dambe. An sami wani karamin yaro da ya ke da shekaru takwas da haihuwa kawai mai suna Peng Jun ya yi wasan dambe har tsawon shekaru hudu a birni Changsha,babban birni na lardin Hunan na kasar Sin. Karamin yaron ya ce burinsa shi ne ya zama dan dambe da zai wakilci kasar Sin shiga wasannin Olympics da sauran wasannin duniya yayin da ya girma. Wannan yaron na cikin makarantar firamare ya ce ba zai daina wasan dambe ba. Shi yaro ne da ya fi kankanta a cikin 'yan wasa da suka shiga wasan dambe a kasar Sin.Ya kan samu horo a karshen kowane mako.

An shirya abincin musamman domin tagwayen Koala a lambun yawon shakatawa. An shirya abincin musamman a lambun yawon shakatawa na Xiangjiang na birnin Guangzhou da ke kudancin kasar Sin domin mata tagwayen dabbobin da ake kiransu "Koala" a turance a ranar da aka haife su. Masu yawon shakatawa da yawa da ma'aikatan gidan kiwo dabbobi sun tsaya a wurin da koala ke wasa sun gadam idanunsu yadda koala sun cin abincin musamman,kuma sun rera wakoki domin su. Mr Sean Kelly,karamin jakada na kasar Australiya a birnin Guangzhou na kasar Sin shi ma yana wurin ya kuma yanke abincin musamman na ranar haihuwa domin dabbobi Koala. A shekara ta 2006 ne gidan kiwo dabbobi ya shiga da koala guda hudu daga kasar Australiya,yawansu ya wuce goma a halin yanzu.(Ali)