Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-01-03 15:07:22    
Wani jami'in diplomasiya na Amurka ya mutu a kasar Sudan sakamakon kisan gillar da aka yi masa

cri
A ran 1 ga wata wani jami'in diplomasiya na Amurka da ke kasar Sudan ya mutu sakamakon kisan gillar da aka yi masa a birnin Khartoum, hedkwatar kasar, wannan ya zama karo na farko ke nan da ska yi wa 'yan diplomasiya kisan gilla cikin 'yan shekarun nan da suka wuce a kasar Sudan.

An yi wannan hargitsin harben bindiga wajen karfe 4 na wannan rana da asuba, a wancan lokaci, wata mota ta ofishin jakadancin Amurka dake tafiya bisa wata muhimmiyar hanya ta birnin Khartoum ta gamu da farmakin daga wajen wasu dakarun da ba a san ko su wane ne ba, wanda ya yi sanadiyar mutuwar direban kasar Sudan, kuma 'yan bindiga sun bindige wani jami'i Ba'amurke na hukumar shirin raya kasa da kasa da ke cikin motar, daga baya an kai shi asibiti, amma ya mutu sakamakon naunukan da ya samu. Har yanzu ba wata kungiya ko wani mutun da suka yi shelar cewa su n dauki alhakin kai wannan hari ba.

Ra'ayoyin bainal jama'a sun bayyana cewa, ba shakka wannan hargitsin ya kara tsananta dangantakar da ke tsakanin Amurka da Sudan wadda da ma ta yi tsanani sosai a tsakaninsu. Tun shekaru 90 na karnin da ya wuce, dangantakar da ke tsakanin Sudan da Amurka kullum kara lalacewa take. Amurka ta zargi gwamnatin Sudan wai ta goyi bayan ta'addancin kasashen duniya, kuma tana yin "kisan gillar kabilu" a shiyyar Darfur. Amma gwamnatin Sudan ta tsaya haikan ta musunta karar da Amurka ta kai mata.

Abin da ya kamata a sa lura a kai shi ne, a jajiberen aukuwar hargitsin mutuwar jami'in diplomasiya na Amurka da ke Sudan sakamakon kisan gillar da aka yi masa, Mr. Bush ya sake sa hannu kan wata doka wadda ta yarda da gwamnatocin jihohi da na hukumoni daban-daban na Amurka da su tsayar da zuba jarinsu ga kamfanoni wadanda ke yin mu'amala da Sudan wajen hakar man futur da sauran albarkatun kasa, a sa'i daya kuma wasu kamfanoni masu zuba jari na Amurka su ma za su iya tsayar da mu'amalar da suke yi da muhimman hukumomin tattalin arziki na Sudan tun kafin lokacin da aka kayyade kuma ba tare da daukar alhakin matsalar bisa wayansu ba.

Amma bayan mutuwar wannan jami'in diplomasiya na Amurka sakamakon kisan gillar da aka yi masa, wasu kafofin watsa labarai sun yi tsammani cewa, wannan hargitsi yana da nasaba da kungiyar Al-Qaida. Sun bayyana cewa, madugun kungiyar Al-Qaida Osama bin Laden da mataimakinsa Ayaman al-Zawahri sun taba yin kira da a tayar da yakin jahadi a kasar Sudan kan kasashen yamma.

Amma, a ranar da wannan jami'in diplomasiya na Amurka ya mutu sakamakon kisan gillar da aka yi masa, ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sudan ta bayar da wata sanarwa cewa, harin nan da aka yi da bindiga ba harin ta'addanci ba ne, amma wani hargitsi ne kawai wanda ba shi da ma'anar siyasa, kuma ba zai jawo mugun illa ga halin da ake ciki a kasar Sudan da dangantakar da ke tsakaninta da sauran kasashe ba. Sanarwar ta nanata cewa, gwamnatin Sudan kullum tana dukufa kan aikin kulawa da kuma kiyaye mutanen kasashen waje da ke cikin kasar, musamman ma 'yan diplomasiya, nan gaba ma za ta ci gaba da yin matukar kokari domin samun tabbaci ga kwanciyar hankali na wadannan mutane. Sassan da abin ya shafa sun riga sun fara bin bahasi kan wannan hargitsin da aka yi da bindiga, ko ba dade ko ba jima za a hukunta masu laifi bisa dokoki. (Umaru)