A shekara ta 2008, birnin Beijing zai dauki jerin matakai don tabbatar da ingancin abinci da za a samar wa mutane fiye da miliyan 16 da ke birnin a lokacin yin gasar wasannin Olympics ta Beijing.
Bisa shirin aiki na shekara ta 2008 da hukumar masana'antu da kasuwanni ta Beijing ta bayar a ran 2 ga wata, an ce, a shekara ta 2008, birnin Beijing zai aiwatar da ka'idojin fasahohin tabbatar da ingancin abinci da za a samar don gasar wasannin Olympics, da kuma ma'aunin shigar da su daga dukkan fannoni. Kuma zai yi bincike kan magunguna masu sa kuzari da ke cikin abinci a tsanake bisa ka'idojin, ta yadda za a yi kokari wajen share fage sosai ga ayyukan yaki da ta'addanci a fannin abinci.
A waje daya kuma, birnin Beijing zai kaddamar da tsarin bincike kan ingancin abinci don gasar wasannin Olympics, ta yadda za a iya tabbatar da samun cikakkun labaru dangane da wuraren samar da abincin da kamfanonin sarrafa da kuma daukar abincin.(Kande Gao)
|