Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-01-02 14:07:24    
Wasan lankwashe-lankwashen fasaha mai tsarin musamman na gargajiyar kasar Sin ya sami babban ci gaba

cri

Kwanakin baya ba da dadewa ba,an kawo karshen gasar wasan lankwashe-lankwashen fasaha ta duniya ta shekarar 2007 da aka shirya bisa gayyata a cibiyar wasan motsa jiki ta jami`ar masana`antu ta Beijing,kungiyar kasar Rasha ta samu dukkan lambobin zinariya na gasa biyu wato gasa ta mutum daya a duk fannoni da gasa ta dukkan `yan wasan kungiya a duk fannoni.Abu mai faranta ran mutane shi ne kungiyar kasar Sin ta samu zama ta uku a gun gasar dukkan `yan kungiya a duk fannoni,dalilin da ya sa haka shi ne domin kungiyar kasar Sin tana mai da hankali kan tsarin gargajiyar kasar Sin,shi ya sa ta sami sakamako mafi kyau a tarihinta.A cikin shirinmu na yau,bari mu kawo muku bayani kan wannan.

A gun gasar cin kofin duniya ta wasan lankwashe-lankwashen fasaha ta duniya ta shekarar 2007,kungiyar kasar Sin ta samu zama ta tara ta gasar dukkan `yan kungiya a duk fannoni.Amma bayan watanni uku kawai,kungiyar kasar Sin ta samu zama ta uku,ina dalilin da ya sa haka?Game da wannan,shugabar kungiyar kasar Sin Zhang Shuo ta bayyana cewa, `Bayan aka kammala gasar cin kofin duniya,sai mun kara kyautata fasaharmu,muna fatan za mu samu sakamako mai gamsarwa,yanzu muna iya cewa mun riga mun cim ma burinmu.`

Wannan gasar da aka shirya bisa gayyata ita ce gasar gwaji ta gasar wasannin Olympic ta Beijing,dukkan kungiyoyi wadanda suka zama 10 na kan gaba na gasar dukkan `yan kungiya a duk fannoni a gun gasar cin kofin duniya ta shekarar 2007 sun shiga wannan gasa,alal misali,kungiyar kasar Rasha da kungiyar kasar Italiya da dai sauransu.Ana iya cewa,matsayin wannan gasa shi ne matsali ya fi koli a duniya.

A gun zagaye na karshe na gasar,kungiyoyi daban daban sun yi takara mai tsanani,kungiyar kasar Sin ita ma ta yi kokari,musmaman a fannin tufafi da kide-kide da kuma fasahar wasa,alal misali,`yan wasan kasar Sin sun yi amfani da siffar dawisu da kide-kiden gargajiyar kasar Sin.Ana ganin cewa,tsarin musamman na gargajiyar kasar Sin ya sa kungiyar kasar Sin ta fi jawo hankulan `yan kallo.A gun gasar wasannin Olympic ta Beijing,kungiyar kasar Sin za ta ci gaba da nace ga wannan salo.Shugabar kungiyar kasar Sin ta bayyana cewa,  `Za a yi gasar wasannin Olympic ta shekarar 2008 a kasar Sin wato a birnin Beijing,shi ya sa za mu zabi kide-kiden gargajiyar kasar Sin don nuna wa `yan kallon duniya tsarin musamman na kasar Sin.`

Kan wannan,shugabar kungiyar kasar Italiya Blanchi Elisa ta bayyana cewa,  `Kungiyar kasar Sin ta yi kokari,muna jin dadi,ko shakka babu su ma suna jin dadi saboda suka samu yabo a kasarsu.`

Kodayake `yan kungiyar kasar Sin suka samu sakamako mai gamsarwa,amma sun gane sosai cewa dole ne su ci gaba da sanya matukar kokari domin kyautata fasaharsu.`Yar wasa ta kungiyar kasar Sin Sui Jianshuang ta bayyana cewa,  `Mun yi kokari,amma dole ne mu ci gaba saboda matsayinmu bai kai na kungiyar kasar Rasha ba.`

`Yar wasa daga kasar Ukraine wadda ta samu zama ta farko ta mutum daya a duk fannoni ta gasar cin kofin duniya ta shekarar 2007 kuma ta samu zama ta biyu ta mutum daya a duk fannoni ta gasar da aka shirya bisa gayyata Anna Bessonova ta bayyana cewa,  `A ganina,`yan wasan kasar Sin sun yi kokari,kamata ya yi su ci gaba da kiyaye tsarinsu,za su samu sakamako mai kyau.`

Yanzu dai,`yan wasan kungiyar kasar Sin suna yin aikin share fage domin shiga gasar wasannin Olympic ta Beijing.shugabar kungiyar kasar Sin Zhang Shuo ta ce,  `Muna da mafarki muna da buri,yanzu muna jiran shekarar 2008 muna jiran gasar wasannin Olympic ta Bejing.`(Jamila Zhou)