Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-01-02 14:05:39    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki (26/12-01/01)

cri

Ran 31 ga watan jiya,cibiyar sayar da tikitin kallon gasa ta kwamitin shirya gasar wasannin Olympic na birnin Beijing ta bayar da wani rahoto inda ta sanar da cewa,an riga an kammala mataki na biyu na aikin karban takardar bukatar sayen tikitin kallon gasar wasannin Olympic a cikin yankin kasar Sin a ran 30 ga watan jiya.Kwamitin shirya gasar wasannin Olympic na Beijing ya sanar da cewa,an riga an kawo karshen mataki na biyu na aikin karban takardar bukatar sayen tikitin kallon gasar wasannin Olympic da tikitin kallon bikin bude da rufe gasar wasannin Olympic ta nakasassu,yanzu dai ana aikin raba tikitin,kuma a wannan lokaci ba za a karban takardar bukatar sayen tikiti ba.Rahoton ya bayyana cewa,bayan na`urar kwakkwarwa ta gama aikin zabe,za a sanar da masu cin nasarar sayen tikiti wadanda suka gabatar da takardar bukatar sayen tikiti ta hanyar shiga tashar internet ta gwamnatin kasar Sin ko zuwa ofisoshin sayar da tikiti na bankin kasar Sin ta hanyar aika da email ko sakon wayar salula ko wasika.Rahoton shi ma ya bayyana cewa,mutane wadanda ke son sayen tikitin kallon gasar za su iya ci gaba da gabatar da takardar bukatar sayen tikitin gasar a watan Afrilu na wannan shekara,a wancen lokaci kuma za a fara mataki na uku na aikin sayar da tikitin.

Ran 29 ga watan jiya,an kafa kungiyoyin kula da dakunan babbar cibiyar watsa labarai wato MPC da cibiyar watsa labarai ta duniya wato IBC na gasar wasannin Olympic ta Beijing,kafuwarsu ta nuna mana cewa,ana gudanar da aikin kafofin watsa labarai na gasar wasannin Olympic ta Beijing lami lafiya.MPC ita ce wurin da `yan jarida da yawansu zai kai 5600 za su yi aiki kuma ita ce wurin da za a yada labarai,ban da wannan kuma MPC za ta nuna wa jama`ar duniya al`adun kasar Sin.Game da IBC kuwa,masu aikin TV da rediyo fiye da dubu goma za su yi aiki a nan.Za a bude kofar MPC da IBC ga `yan kallo a ran 8 ga watan Yuli na shekarar 2008.

Ran 28 ga wata,a birnin Beijing,mataimakin shugaban zartaswa na kwamitin shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing Jiang Xiaoyu ya fayyace cewa,an riga an kammala aikin gina filin wasan motsa jiki mai siffar `Tafkin Wanka` wato `Water Cube` wanda shi ne gini mai alamar gasar wasannin Olympic ta Beijing,a halin da ake ciki yanzu,ana yin aikin share fage domin shirya gasar gwaji ta gasar wasannin Olympic ta Beijing a wannan wata.Jiang Xiaoyu ya kara da cewa,ana tafiyar da aikin gina dakuna da cibiyoyi na gasar wasannin Olympic ta Beijing yadda ya kamata. (Jamila Zhou)