Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-01-02 13:02:14    
Zama lafiya ya samar da bunkasuwa ga kasar Uganda

cri

A 'yan shekarun baya, kasar Uganda ta samu bunkasuwa sosai kan harkokin tattalin arziki, nasarorin da ta samu su ne, yawan karuwar tattalin arzikin da kasar Uganda ta samu a cikin jerin shekaru 15 da suka gabata ya kai kashi 6 daga cikin dari, yawan ayyukan gona a duk harkokin tattalin arzikin kasar ya kara raguwa, kasar Uganda ta riga ta fara kaddamar da masana'antu, kuma yawan matalauta a kasar ya kara raguwa. Dalilin ya sa aka haddasa haka shi ne, zaman lafiya da aka shimfida a kasar Uganda, muna iya ganin cewa, zaman lafiya ya samar da bunkasuwa ga kasar Uganda.

A yankin da ke arewacin kasar Uganda, yakin basasa da aka yi cikin shekaru 20 ya lalata tattalin arziki sosai. Amma a watan Yuli na shekarar 2006, an cimma burin shimfida zaman karko a arewacin kasar Uganda. Gwamnatin kasar ta fara sa kaimi ga 'yan gudun hijira da su koma gida, domin sake gudanar da aikin gona, haka kuma gwamnatin kasar Uganda ta ba su kayayyakin noma da ire iren amfanin gona. A sabo da haka ne, tattalin arziki a wannan yanki ya fara samun bunkasuwa.

A farkon shekarar 2005, an samu sulhuntawa a tsakanin bangarorin kudu da arewa na kasar Sudan, a sakamakon haka, an shimfida zama karko a kudancin kasar Sudan. Gwamnatin kasar Sudan kuma ta fara sake gina kasar bisa babban mataki, yawan saye da sayarwa da aka yi a yau da kullum ya karu da gaske. A lokacin, farashin kayayyakin kasar Sudan ya ninka sau uku ko biyar idan aka kwatanta shi da na kasar Uganda. Sabo da hake ne, 'yan kasuwa na kasar Uganda suka je kasar Sudan domin tafiyar da harkokinsu, haka kuma cinikayya da ke tsakanin kasar Uganda da kudancin kasar Sudan ya kara samun bunkasuwa.

Ko da yake kasuwar kasar Uganda karama take yi, amma tana makwabataka da kasashen Sudan, da Kongo(Kinshasa), da Ruwanda, da kuma Tanzaniya. Idan kasar Uganda tana zama karko, za ta iya samun damar samun bunkasuwar tattalin bisa matsayinta na hada sauran kasashe.

A karshen shekaru 90 na karnin da ya gabata, kasar Uganda ta taba tura sojoji zuwa kasar Kongo(Kinshasa), domin nuna goyon baya ga 'yan hamayya na kasar Kongo(Kinshasa), sabo da haka ne, kasashen biyu sun yi adawa da juna sosai.

Amma tun daga shekarar 2007, kasashen biyu wato Uganda da Kongo(Kinshasa) sun dauki hakikanan matakai da samun sulhuntawa. Shugabanni na kasashen biyu kuma sun gana da juna kan harkokin iyakar kasa, haka kuma sun yanke shawarar yin shawarwari, kan yin amfani da albarkatan mai da gas cikin hadin gwiwa, da sake tabbatar da iyakar kasa a tsakaninsu, da kuma kawar da 'yan tawaye nasu na kansu da ke sauran kasashensu da dai sauran batutuwa.

A halin yanzu dai, abokan gaba da gaba na da wato kasashen Uganda da Kongo(Kinshasa) sun more makamashi da raya harkokinsu cikin hadin gwiwa, lallai, wannan ya bayyana basirar siyasa ta shugabanninsu. Haka kuma wannan ya nuna mana cewa, muddin a shimfida zaman lafiya a cikin gida da shiyya shiyya kawai, za a iya samun bunkasuwa. A nan gaba kuma, kasar Uganda za ta ci gaba da samun bunkasuwa dbisa fa'idar da zaman lafiya ya kawo mata.(Danladi)